A karon farko Buhari ya sanya takunkumin rufe fuska yayin tafiyarsa zuwa kasar Mali

A karon farko Buhari ya sanya takunkumin rufe fuska yayin tafiyarsa zuwa kasar Mali

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuli, ya kafa tarihin a birnin Bamako

- A karon farko shugaban kasar ya sanya takunkumin rufe fuska yayin da ya sauka a babban birnin kasar Mali

- Buhari ya tafi kasar Mali ne domin kwantar da tarzoma da sulhunta rikicin siyasa da ta mamaye kasar Mali tun bayan babban zaben kasar da aka gudanar

A karo na farko tun bayan da cutar korona ta bulla a Najeriya fiye da watanni hudu da suka gabata, an hangi shugaban kasa Muhammadu Buhari sanye da takunkunmin rufe fuska a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuli.

Shugaba Buhari ya bayyana karo na farko a fili sanye da takunkumin rufe fuska yayin da ya sauka a Bamako, babban birnin kasar Mali.

Babu shakka sanya takunkumin rufe fuska na daya daga cikin muhimman ka'idodin da mahukuntan lafiya suka shar'anta domin dakile yaduwar cutar korona.

Buhari yayin da ya sauka a birnin Bamako
Hoto daga fadar shugaban kasa @BashirAhmaad
Buhari yayin da ya sauka a birnin Bamako Hoto daga fadar shugaban kasa @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Hoto daga fadar shugaban kasa @Buharisallau1
Buhari yayin da ya sauka a birnin Bamako Hoto daga fadar shugaban kasa @Buharisallau1
Asali: Twitter

Buhari yayin da sauka a birnin Bamako
Hoto daga fadar shugaban kasa @Buharisallau1
Buhari yayin da sauka a birnin Bamako Hoto daga fadar shugaban kasa @Buharisallau1

Sai dai ko sau guda ba a taba ganin shugaba Buhari ya sanya takunkumin rufe fuskar ba duk da kuwa yana karbar baki a fadarsa ta Villa tare da halartar muhimman taruka da suka shafi kasar kamar zaman majalisar zartarwa na mako-mako.

KARANTA KUMA: An kammala ƙera motocin farko masu amfani da wutar lantarki a Najeriya

Tare da sauran shugabannin kasashen yankin Afrika ta Yamma wanda shugaban Nijar Muhammadou Issofou ya jagoranci tawagarsu, Buhari ya ziyarci birnin Bamako ne domin sulhunta rikicin siyasa da ya addabi kasar.

Shugaba Buhari ya bar Najeriya ne tare da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, inda suka dira a birnin Bamako da safiyar yau ta Alhamis da kuma wasu daga cikin shugabannin Kungiyar raya Tattalin Arzikin Afirika Ta Yamma (ECOWAS).

Sauran shugabannin kasar da suka dira a birnin Bamako da wannan manufa sun hadar da na Ghana; Addo Nana Akuffo-Addo; shugaban Senegal, Macky Sall da kuma shugaban kasar Cote d'Ivoire, Alasanne Ouattara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng