NDDC: Majalisar Wakilai za ta maka Akpabio a kotu

NDDC: Majalisar Wakilai za ta maka Akpabio a kotu

Majalisar Wakilai ta Tarayya ta yi barazanar yin karar Ministan Niger Delta Godswill Akpabio a kotu kan ikirarin da ya yi na cewa kaso mai yawa cikin kwangilolin hukumar NDDC, yan majalisan ne aka bawa.

Ministan ya yi wannan ikirarin ne yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar da aka kafa domin duba kudaden da ake kashewa a hukumar ta NDDC da ake ganin ya wuce hankali.

Daily Trust ta ruwaito cewa Majalisar, a zaman ta na ranar Talata, ta kallubalanci ministan ya wallafa sunayen yan majalisar da ya yi ikirarin sun karbi kwangilar a NDDC.

NDDC: Majalisar Wakilai za ta maka Akpabio a kotu
Godswill Akpabio
Asali: UGC

Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila, a ranar Alhamis ya ce Majalisar za ta garzaya kotu tayi karar Akpabio muddin ya gaza kawo hujja a kan ikirarin da ya yi a baya.

DUBA WANNAN: An bawa Sarkin Shinkafi wa'addin awa 24 ya kwace sarautar da ya bawa Fani-Kayode

A baya Legit.ng ta kawo muku cewaFemi Gbajabiamila ya bawa Godswill Akpabio, wa'adin awa 48 ya wallafa sunayen 'yan majalisa zubi na 9 da suka karbi kwangila daga NDDC.

Kakakin ya yi wannan jawabin ne lokacin da ya ke martani a kan batun da shugaban marasa rinjaye, Ndudi Elumelu ya gabatar masa.

Mr Elumelu ya bukaci Majalisar ta gayyaci Mr Akpabio ya bayyana sunayen wadanda suka karbi kwangila daga NDDC.

Mr Akpabio a ranar Litinin yayin zaman sauraron baasi game da binciken zargin rashawa a NDDC ya yi ikirarin cewa NDDC na bawa yan majalisa kwangila.

Wannan batun ya tayar da hankula a wurin taron har sai da shugaban taron, Thomas Ereyitomi ya lalashe wasu 'yan majalisa da suka fara cacar baki da ministan.

Da ya ke martani a kan batun da Mr Elumelu ya gabatar masa, Kakakin ya ce bai ji dadin yada 'yan jarida suke taya shi yayata "abinda muka san ba gaskiya bane."

"Ban taba karbar kwangila ba ko sau daya daga NDDC kuma na san wasu yan majalisar da dama kamar ni," in ji Gbajabiamila.

"Saboda haka ina kira ga ministan ya wallafa sunayen yan majalisun, kwangiloli, kwanan wata da kamfanonin da ya ce an bawa kashi 60 na kwangilar ta hukumar NDDC."

Ya ce idan ko ministan bai wallafa sunayen ba majalisar ba ta da wani zabi da ya wuce su dauki matakin da doka ta tanada a kan shi.

"Haka ta rataya a kan ministan, ya sanar da kwamitin, mutanen Niger Delta da 'yan Najeriya wadanda aka bawa kwangilolin," a cewar Kakakin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel