Babu gudu babu ja da baya kan yi wa Fani–Kayode sarauta – Masarautar Shinkafi

Babu gudu babu ja da baya kan yi wa Fani–Kayode sarauta – Masarautar Shinkafi

Masarautar Shinkafi ta Jihar Zamfara ta ce ba za ta soke sarautar da ta yi wa tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani Kayode ba da Sarki, Alh. Muhammad Makwashe ya yi masa duk da masu sarauta 5 sun tube rawunansu.

Wasu daga cikin wadanda suka ajiye sarautarsu sun hada da Dr Suleiman Shinkafi 'Sarkin Shanun Shinkafi' da Dr Tijjani Shinkafi 'Sarkin Marayun Shinkafi'.

A karshen makon da ta gabata ne sarki ya yi wa Fani-Kayode wanda mamba ne na PDP sarautar “Sadaukin Shinkafi” sai dai wasu daga cikin 'ya'yan masarautar ba su amince da hakan ba.

Babu gudu babu ja da baya kan yi wa Fani–Kayode sarauta – Masarautar Shinkafi
Femi Fani Kayode. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

Sai dai, Wamban Shinkafi, Dr Sani Abdullahi da ya yi magana a madadin masarautar ya shaidawa The Punch a ranar Laraba cewa ba za a soke sarautar da aka bawa Fani Kayode ba.

Abdullahi ya ce nan ba da dadewa ba za a maye gurbin masu sarautan biyar da suka tube rawunansu inda ya yi ikirarin cewa dama yan uwa ne da magoya bayan tsohon gwamnan jihar Abdulaziz Yari jigo na APC.

Hakan na nufin cewa rashin amincewar da suka yi da nadin sarautar da aka yi wa Fani Kayode na da alaka da siyasa kenan.

A baya bayan nan, kafin ayi masa sarautar, Fani Kayode ya cacaki Yari saboda rashin bin dokokin dakile yaduwar cutar korona a filin tashi da saukan jiragen sama.

DUBA WANNAN: An bawa Sarkin Shinkafi wa'addin awa 24 ya kwace sarautar da ya bawa Fani-Kayode

Abdullahi ya ce, "Babu yadda za ayi a soke sarautar da aka yi wa Cif Fani Kayode. Sarkin mu mutum ne mai gaskiya. Baya magana biyu. Wannan shine tsarinsa. Haka aka yi masa tarbiyya.

"Hurumin sarki ne bayar da sarauta. Mu kan bawa kowa sarauta, musulmi, kirista, ibo, ko bayarebe ko itsekiri. Mun san dalilin da yasa ake adawa da nadin sarautar. Abin ya samo asali ne daga tsohon gwamnan Zamfara. Duk wadanda suka ajiye sarautarsu suna da alaka da tsohon gwamnan."

Da aka masa tambaya kan dalilin da yasa aka yi wa Fani Kayode sarautar, Abdullahi ya ce tsohon ministan ya samu nasarori da dama kuma ya fito daga babban gida na Cif Remi Fani Kayode (SAN).

Ya kuma ce an yi wa mutane da dama sarauta a arewa kamar tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha, Jagoran APC, Bola Tinubu, tsohon gwamnan Abia, Orji Kalu da mataimakin shugaban kasa Osinbajo.

"Babu kiyayya tsakanin musulmi da kirista ko yan kudu da arewa amma wasu na neman tayar da husuma suna saka siyasa cikin lamarin. An yi masa sarauta ne don kara dankon zumunci. Ya yi minista kuma ya wakilci dukkan Najeriya," inji Abdullahi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel