Basarake ya yi garkuwa da kansa don gudun kada 'Yan sanda su kama shi a Nasarawa

Basarake ya yi garkuwa da kansa don gudun kada 'Yan sanda su kama shi a Nasarawa

Wani mai sarautar gargajiya, Ardon Udege, Alhaji Muhammad Dankawo ya yi garkuwa da kansa domin gudun kada 'yan sanda su kama shi a jihar Nasarawa.

An ruwaito cewa wasu yan bindiga sunyi awon gaba da basaraken a karamar hukumar Udege da ke jihar ta Nasarawa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda suka yi garkuwa da shi sun nemi a biya Naira miliyan 7 kafin su sako shi.

Basarake ya yi garkuwa da kansa don gudun kada hukuma ta kama shi
Basarake ya yi garkuwa da kansa don gudun kada hukuma ta kama shi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An bawa Sarkin Shinkafi wa'addin awa 24 ya kwace sarautar da ya bawa Fani-Kayode

Amma kwamishinan rundunar yan sandan jihar, Mr Bola Longe ya karyata batun garkuwa da basaraken.

Ya ce, "Ba garkuwa da wannan mutumin aka yi ba. Muna neman shi domin mu kama shi. Mun taba kama shi a baya saboda zarginsa da bawa masu garkuwa da mutane bayanai."

Da aka tuntube shi don jin ta bakinsa, shugaban karamar hukumar, Alhaji Muhammed Otto bai daga wayar tarho dinsa ba.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, Gidan Rediyon Freedom ya ruwaito cewa, ɗiyar ɗan majalisar da aka yi garkuwa da ita a Kano, Juwairiyya Murtala, ta kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, Juwairiyya ta koma gidan mahaifinta da ke Unguwar Kore a karamar hukumar Dambatta da misalin uku na daren ranar Talata.

Wani ɗan uwan Juwairiyya, Nura Yusha'u Kore, shi ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai da cewa ta dawo gida cikin koshin lafiya.

A ranar Asabar da din da ta gabat ne masu garkuwa da mutane suka sace 'yar gidan ɗan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Dambatta, Alhaji Murtala Musa Kore.

Masu ta'adar garkuwar sun yi awon gaba da budurwar mai shekaru 17 a duniya yayin da suka yi yunkurin yin garkuwa da mahaifinta wanda ba su riska ba a gida.

Don haka suka tasa ƙeyar Juwairiyya wadda ɗalibar aji biyar ce a makarantar Sakandire ta GSS Jogana kuma ita ce 'yar auta a wurin mahaifinta kamar yadda sashen Hausa na BBC ya ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel