Funtua ya goyi bayan ba wa mata muƙami a gwamnatin Buhari - Aisha Buhari

Funtua ya goyi bayan ba wa mata muƙami a gwamnatin Buhari - Aisha Buhari

Uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta magantu a kan rawar da marigayi Mallam Isma'il Isa Funtua ya rika taka wa a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Hajiya Aisha a ranar Laraba, ta fayyace yadda Marigayi Mallam Funtua ya jajirce wajen goyon bayan mata masu damawa a harkokin siyasa musamman a tsawon shekaru hudun da suka gabata.

Uwargidan shugaban kasar ta ce Marigayi Funtua ya rika faɗi-tashin ganin an bai wa mata akalar jagoranci a Hukumomi da Cibiyoyi a gwamnatin Buhari.

Matar shugaban kasar ta bayyana hakan ne cikin wani sakon na alhini kan mutuwar Mallam Funtua da ta wallafa a shafukanta na dandalan sada zumuta.

Mallam Funtua wanda ya kasance aminin shugaban kasa Buhari, ya yi gamo da ajali ne a ranar Litinin a sakamakon bugun zuciya kamar yadda wani makusancinsa ya bayyana.

Aisha Buhari
Aisha Buhari
Asali: UGC

Aisha Buhari ta ce za a rika tunawa da Funtua saboda goyon bayan da ya rika bai wa mata ‘yan siyasa wajen ganin su rike madafan iko.

Ta rubuta cewa: "Inna lillahi Wa inna ilaihi Raji’un; ma'ana daga Allah muke, kuma gare shi zamu koma."

"A madadin dukkanin iyalina, ina mika sakon ta'aziya ga Hajiya Hauwa Isa Funtuwa da duk iyalinsa Marigayi Mallam Isma'ila Isa Funtua ta wannan babban rashi da suka yi."

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya sa Aljannatul Firdausi makomarsa."

"Ba za a manta da Mallam Isma'ila Isa Funtua saboda goyon bayan mata 'yan siyasa musamman rawar da ya taka wajen ganin sun samu naɗin mukamai a Hukumomi daban-daban tsawon shekaru hudu da suka gabata."

KARANTA KUMA: An sako ɗiyar ɗan majalisar da aka yi garkuwa da ita a Kano

"Muna rokon Allah ya bai wa iyalinsa hakurin juriyar wannan babban rashi da suka yi, Amin."

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Marigayi Funtua yana daya daga cikin mutum uku da suka rike babban ginshiki a gwamnatin Buhari.

Sauran biyun sun hadar da tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban, Marigayi Abba Kyari da kuma ɗan yayar Buhari, Mallam Mamman Daura.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng