Buhari ne shugaba a Afrika da ya fi farin jini a Twitter — Rahoto

Buhari ne shugaba a Afrika da ya fi farin jini a Twitter — Rahoto

Burson Cohn and Wolfe, BCW, kamfanin sadarwa ta duniya cikin kiddigar da ta yi na Twiplomacy ta ce Shugaba Muhammadu Buhari shine ke da mabiya mafi yawa a Twitter cikin shugabanin kasaseshen Afirka.

Kamfanin ta bayyana hakan ne cikin sabon rahotonta na nazarin Twiplomacy na shekarar 2020 inda ta ce Buhari yana da mabiya 3,121,169 a shafin na Twitter.

A cewar nazarin, Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari shine kan gaba wurin yawan mabiya da tazara mai yawa a yankin na Afirka sai mai biye masa Paul Kagame na Ruwanda mai mabiya 1,910,159.

Buhari ne shugaba a Afrika da ya fi farin jini a Twitter — Rahoto
Muhammadu Buhari. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

Ta kuma ce shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa shine wanda ya fi samun mabiya cikin kankanin lokaci a shekarar da ta gabata inda jimillar mabiyansu yanzu 1,386,849.

Nazarin na Twiplomacy ya nuna cewa shugaban Amurka, Shugaba Donald Trump shine shugaba da ke da mabiya mafi yawa a duniya a Twitter inda ya ke da mabiya miliyan 81.1 a shafinsa na @realDonaldTrump.

DUBA WANNAN: Neman sauke hafsoshin tsaro: Buhari ya 'watsa wa ƴan majalisa kasa a ido'

Ta kuma ce Farai Ministan Indiya, Narendra Modi, shine ke biye da Trump da mabiya miliyan 57.9 sai Fafaroma Francis da ke da mabiya miliyan 51 a shafukansu tara masu mabanbantan harsuna.

A cewar rahoton, shugaban Faransa, Emmanuel Macron shine ke da mabiya mafi yawa cikin shugabannin kasashen nahiyar Turai da mabiya 5,293,346 sai Elysée Palace da mabiya 2,492,468.

Rahoton ya ce Farai Ministan Spain, Pedro Sánchez, shine na uku a nahiyar Turai da mabiya 1,405,481.

Har wa yau, rahoton na BCW ya bayyana cewa coronavirus ce batun da shugabanin kasashen duniya suka fi tattaunawa a kai.

Da ya ke tsokaci a kan lamarin, Chad Latz, Babban Jami'in Kirkire Kirkire a BCW, ya ce coronavirus ce babban maudu'in ta aka fi tattaunawa a Twitter cikin makonni uku da suka gabata.

Latz ya ce saboda dokar kulle da aka saka a kasashen duniya, mutane da dama sun koma mayar da hankali a Twitter kuma shugabannin duniya suna amfani da shi domin fadakar da al'ummarsu game da cutar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel