Gwamnoni 8 a Najeriya da suka harbu da cutar korona

Gwamnoni 8 a Najeriya da suka harbu da cutar korona

Bayan fiye da watanni hudu kenan da bullar cutar korona karo na farko a Najeriya, cutar mai toshe kafofin numfashi ta yadu a jihohi 36 da kuma babban birnin kasar na Tarayya wato Abuja.

Wannan ya na kunshe cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a daren ranar Talata, 21 ga watan Yuli.

Alamu na nuna cewa annobar Coronavirus ba ta duban isa, girma ko mulki.

Hakan a bayyana yake idan aka duba irin mutanen da cutar ke damka a Najeriya.

A yau Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti ya shiga sahun gwamnonin Najeriya da cutar ta kama.

Fayemi ya sanar da hakan ne a shafinsa na Twitter inda yace ya mika mulkin jihar na wucin-gadi ga mataimakinsa, Adebisi Egbeyemi.

Amma kuma, gwamnan jihar Ekiti ba shine gwamna na farko da ya kamu da cutar ba a jerin 'yan siyasar Najeriya.

Gwamnoni 8 a Najeriya da suka harbu da cutar korona
Gwamnoni 8 a Najeriya da suka harbu da cutar korona
Asali: UGC

Ga jerin gwamnonin da suka yi fama da muguwar annobar da ta zama ruwan dare dame duniya:

1. Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti

2. Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi.

3. Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia.

4. Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta.

5. Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo.

6. Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.

7. Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi.

8. Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar Aso Rock

A wani bangare, Legit.ng ta ruwaito yadda hankalin jama'ar jihar Ekiti ya matukar tashi bayan da aka tabbatar da cewa Gwamna Fayemi na dauke da cutar bayan ganawar da yayi da wasu mutum biyu da aka tabbatar sun harbu.

Fayemi ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a safiyar Laraba wurin karfe 10:25 na safe.

A halin da ake ciki, hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 576 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:56 na daren ranar Litinin 21 ga Yulin shekarar 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel