Yanzu: Majalisar dattijai ta ba Buhari nan da Satumba ya gabatar da kasafin 2021

Yanzu: Majalisar dattijai ta ba Buhari nan da Satumba ya gabatar da kasafin 2021

Rahoton da Legit.ng Hausa ke samu daga jaridar Punch na nuni da cewa shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gabatar da kasafin kudin kasar na 2021 kafin nan da watan Satumbar wannan shekarar.

Lawan ya bayyana hakan a lokacin da yake tsokaci kan takardar hasashen kasafin 2021-2023 MTEF/FSP, da shugaban kasar ya gabatarwa majalisar a ranar Talata.

Shugaban kasar ya gabatar da wannan takardar ne domin baiwa majalisar damar daukar matakin da ya dace, wanda kuma yasa majalisar ta a yanzu ta bashi wannan wa'adi.

Shugaban majalisar dattijan ya ce gabatar da kasafin 2021 kafin watan Satumba, zai taimakawa majalisar wajen daukar mataki da kuma sa hannu kan kasafin kafin karshen watan Disamba.

Ya kuma bukaci kwamitoci daban daban da abun ya shafa da su tuntubi kwamitocin tattara haraji domin tabbatar da cewa aikin kasafin kudin ya tafi kamar yadda ya kamata.

Cikakken labarin yana zuwa....

KARANTA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta gabatar da N12.7tr a matsayin kasafin 2021 na kasar

Yanzu: Majalisar dattijai ta ba Buhari nan da Satumba ya gabatar da kasafin 2021
Yanzu: Majalisar dattijai ta ba Buhari nan da Satumba ya gabatar da kasafin 2021
Asali: Facebook

A ranar Talata, Gwamnatin tarayya ta ce tana hasashen gabatar da N12,658,009,802,283.00 a matsayin kasafin kudin kasar na 2021.

Gwamnatin ta ware N5.16trn a matsayin rarar kasafin na 2021 wanda ya haura N4.98trn da aka samu a kasafin 2020.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar taswirar kasafin mai taken MTEF/FSP wacce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatarwa majalisar dattijai a ranar Talata.

Gwamnatin tarayyar ta kuma tsayar da kudin danyen mai na shekarar 2021, $40 akan kowacce gangar mai da kuma canjin N360 akan kowacce dala.

A cewar takardar, kudaden da aka yi hada hadarsu sun kai N481bn, ana bin kasar bashin N3.12trn, sai kudin da aka ware don biyan bashin N220bn da kuma N5.7 kudin fansar kaya da ayyuka.

Gwamnatin ta kuma ware N3.33trn a matsayin kudaden da aka ware don gudanar da ayyukan kasar.

Gwamnatin na hasashen samun N500bn daga bangaren kudaden harajin sitamfi, sabanin N200bn da aka samu a shekarar 2020.

Gwamnatin ta yi nuni da cewa an ware N4.31 a matsayin kudaden jami'ai da fansho, karin N724.67bn akan na shekarar 2020.

Kudaden jami'ai, na ci gaba da karuwa a kowacce shekara sakamakon yawaitar daukar ma'aikata da hukumomin gwamnati ke yi, wasu lokutan ba tare da bin ka'ida ba.

Gwamnati tayi gargadin cewa bisa hasashen kashi 70 na harajin da za a tattara na 2021, ba lallai bane a iya biyan kudaden jami'an. Gwamnatin ta kuma yi hasashen hako ganga 1.88m ta danyen mai a kowacce rana a 2021 sabanin 1.80mbpd na kasafin shekarar 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel