Shagalin babbar sallah: JNI ta bai wa Musulmin Najeriya shawara

Shagalin babbar sallah: JNI ta bai wa Musulmin Najeriya shawara

- Kungiyar Jama'atu Nasril Islam ta bada muhimmiyar shawara ga Musulmi a yayin da shagalin babbar sallah yake gabatowa

- Kungiyar Musuluncin ta yi kira ga Musulmi da su yi shagalin babbar sallah a cike da natsuwa da tsafta

- Khalid Abubakar Aliyu, sakatare janar na kungiyar Jama'atu Nasril Islam, ya yi kira ga jama'ar Musulmi da ke fadin kasar nan da su kiyaye yayin shagalin bikin babbar sallah

Kungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI) ta shawarci Musulmi da su yi shagalin bikin babbar sallah cikin lumana tare da zaman lafiya tare da nesa-nesa da juna don gujewa cunkoso.

Daily Trust ta ruwaito cewa wannan ya fito ne daga sakatare janar na kungiyar, Khalid Abubakar Aliyu, wanda ya fitar a ranar Talata, 21 ga watan Yuli a Kaduna.

Ya kara da shawartar Musulmi da su kiyaye mu'amalarsu a yayin idin nan da kuma bayan nan.

Legit.ng ta ruwaito cewa, JNI ta yi kira ga dukkan jama'ar Musulmi na Najeriya da su dage da addu'a a cikin kwanaki 10 farkon watan Dhul-Hijjah wanda akwai yuwuwar ya fara daga ranar Laraba, 22 ga watan Yulin 2020.

Shagalin babbar sallah: JNI ta bai wa Musulmin Najeriya shawara
Shagalin babbar sallah: JNI ta bai wa Musulmin Najeriya shawara Hoto: The Cable
Asali: UGC

"Wasu daga cikin ayyukan da ake bukatar Musulmi ya aikata na ambaton Allah mai girma da daukaka sune, karatun Qur'ani, Istigfari, biyayya ga iyaye, kyautatawa 'yan uwa, sadaka ga mabukata, tausayi, sasanci da kuma ziyartar marasa lafiya.

"Mu yi amfani da wannan damar wurin neman tafiyar Allah tare da bauta masa don ya kawo karshen kalubalen da ya addabi kasar nan," yace.

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar ya soke bukukuwan babbar Sallar Layya a jihar.

Ya kuma dakatar da sarakuna biyar masu daraja na jihar daga jagorantar duk wani hawan Sallah ko hawan daushe a babbar Sallar wannan shekarar.

Gwamnan ya bayar da wannan umurnin ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.

A tattaunawar, ya ce wannan umurnin na daga cikin yunkurin gwamnatin jihar na ci gaba da yaki don dakile yaduwar cutar COVID-19.

Ya bayyana cewa, jihar a yanzu ta samu gagarumar nasara ta wannan fuskar, kasancewar bata samu bullar cutar ba kusan kwanaki 30 yanzu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel