'Yan bindiga sun halaka dagaci da mutum tara a Kaduna

'Yan bindiga sun halaka dagaci da mutum tara a Kaduna

'Yan bindiga sun kashe dagajin kauyen Gora Gan da ke karamar hukumar Zangon Kataf na jihar Kaduna da wasu mutane tara.

Wannan na zuwa na kimanin awa 24 bayan kashe wasu matasa 21 yayin bikin daurin aure a kauyen Kukum Daji da ke karamar hukumar Kaura.

The Nation ta ruwaito cewa har da wani yaro mai shekara shida cikin wadanda aka kashe a harin na baya bayan nan tare da jikkata wasu mutane da dama.

Wani wanda abin ya faru a idonsa ya ce yan bindiga kimanin su 20 ne suka kai farmaki kauyen misalin karfe 7 na yamma a ranar Litinin suka fara harbe harbe.

'Yan bindiga sun halaka dagaci da mutum tara a Kaduna
'Yan bindiga sun halaka dagaci da mutum tara a Kaduna. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Mataimakin shugaban kungiyar Kirista ta Najeriya, CAN, reshen karamar hukumar Zangon LKataf, Fasto Isaac Ango-Makama ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce an kone gidaje da dama yayin harin.

DUBA WANNAN: Wani ya kashe kansa a harabar ofishin hukuma saboda tarar N215,000

Ya ce an kai gawarwakin wadanda suka mutun zuwa babban asibitin garin Zonkwa yayin wadanda suka jikkata kuma an kai su wani asibitin inda ake musu magani.

"Wasu daga cikin mazauna kauyen har yanzu sune neman wasu daga cikin yan uwansu da ba a gano su ba," in ji faston.

Sakataren Sansanin Yan Gudun Hijira ta Mercy da ke Zonkwa, Ezekiel James ya ce suna matukar neman tallafi domin su kula da wadanda suka rasa muhallansu.

James ya kara da cewa ana samun karuwan mutane a sansanin duba da yadda ake kai hare hare sosai a kauyukan da ke makwabtaka da su.

Jamiyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Kaduna ta yi Allah wadai da harin inda ta ce ba yawan hare haren da ake kaiwa a kudancin Kaduna ya kazanta.

Sakataren watsa labarai na jamiyyar, Abraham Catoh, cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce gwamna Nasir El Rufai baya daukan matakan da suka dace domin ganin an magance matsalar rashin tsaro a jihar.

Mai magana da yawun Rundunar Yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige bai amsa kirar da aka yi masa ba ta wayar tarho ne neman jin ba'asi a game da sabon harin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel