Sama Isa: Labarin Amini kuma Surukin Buhari, tsohon Minista da ya cika

Sama Isa: Labarin Amini kuma Surukin Buhari, tsohon Minista da ya cika

A cikin farkon makon nan ne aka wayi gari a Najeriya da labarin mutuwar Isma’ila Isa Funtua, wanda aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma surukinsa.

Legit.ng Hausa ta kawo maku takaitaccen tarihin wannan Bawan Allah da ya cika a ranar Litinin.

1. Haihuwa

An haifi Ismaila Isa Funtua OFR, mni ne a Junairun shekarar 1942 kamar yadda shafinsa na Wikipedia ya nuna. An haife shi a garin Funtua da ke cikin kudancin jihar Katsina.

2. Karatu

Ismaila Isa ya fara karatunsa a garin Funtua inda ya halarci makarantun addini, ya koyi ilmin Al-qur’ani, fikihu da hadisan Manzon Allah SAW.

A bangaren boko kuwa, ya halarci kwalejin koyon kasuwanci ta Zariya, da wata cibiyar horaswa a Kaduna. Daga baya ya yi karatu a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya kuma yi karatu a jami’ar Manchester da ke Ingila.

Funtua ya na cikin daliban makarantar manyan ma’aikata ta NIPS da ke Kuru.

3. Aiki

Isa Funtua ya fara aiki da ma’aikatar En’E ta jihar Katsina da gwamnatin Arewa. Daga baya ya zama shugaba a kamfanin United Textiles Limited a Kaduna da ma’aikata a karkashinsa.

Funtua ya kafa gidan jaridar The Democrats a 1983 a Kaduna, daga cikin wadanda ya yi aiki da su har da Marigayi Malam Abba Kyari, har ya kuma rike shugaban kungiyarsu ta NPAN.

Bayan ya yi ritaya daga aiki, Isa Funtua ya bude kamfanin gine-gine na Bullet Construction.

KU KARANTA: Shugaban kasa ya yi jawabi bayan Ismaila Isa Funtua ya kwanta dama

Sama Isa: Labarin Amini kuma Surukin Buhari, tsohon Minista da ya cika
Samaila Isa Funtua
Asali: Twitter

4. Gwamnati

Marigayi Ismail Isa Funtua ya shiga siyasa a 1978, ya kuma yi dacen zama ministan ruwa a gwamnatin NPN. A wancan lokaci Funtua ne ‘dan auta cikin ministocin shugaba Shehu Shagari.

A 1994 Ismail Isa Funtua ya samu shiga cikin babban taron kasa da Janar Sani Abacha ya shirya. Ana zargin cewa Gwamnatin sojin Janar Sani Abacha ta sa Isa Funtua a cikin makiyanta.

5. Iyali

Ismaila Isa Funtua ya na auren 'diyar Lamidon Adamawa da ya rasu, ya na dangantaka da Marigayi tsohon Wazirin Katsina Isa Kaita.

Daga cikin ‘ya ‘yansa akwai Abubakar Ismaila Isa Funtua wanda ke auren 'diyar shugaban kasa, Safinatu Muhammadu Buhari.

Abubakar Ismaila Isa Funtua ‘dan siyasa ne wanda ya ke harin kujerar gwamna a jihar Katsina.

Daga cikin ‘yanuwan Marigayin akwai Farfesa Idris Isa Funtua, tsohon shugaban jami’ar Ummaru Musa ‘Yaradua, Katsina.

6. Mutuwa

A daren Litinin, 20 ga watan Yuli, 2020 Ismaila Isa Funtua ya mutu. Ana zargin cewa zuciyarsa ce ta buga bayan ya bar gida ya fadawa iyalinsa zai je ganin likita, kafin ya karasa asibiti, ya tsaya wajen wanzaminsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel