Yadda Duniya za ta tuna da tsohon Aminin Buhari, Ismaila Isa Funtua

Yadda Duniya za ta tuna da tsohon Aminin Buhari, Ismaila Isa Funtua

A ranar Litinin, 20 ga watan Yuli ne aka samu labarin cewa Ismaila Isa Funtua ya samu faduwar gaba, wanda wannan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Legit.ng Hausa ta binciko yadda kwanakin karshen tsohon Ministan tarayyar kasar su ka kare.

Mayu 2019

A cikin watan Mayun bara ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi aikin Umrah a Saudi Arabiya. Daga cikin wadanda su ka yi masa rakiya har da na kusa-da-shi, Ismaila Isa Funtua.

Satumban 2019

A cikin watan Satumba, jama’a sun ga Marigayi Isa Funtua a kotun koli da ke Abuja, inda ya halarci shari’ar zaben shugaban kasa da ake yi tsakanin Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar.

Marigayin ya zauna ne shiru ya ne rike da wayarsa, tare da su Mamman Daura da Nuhu Ribadu

Junairun 2020

A farkon shekarar nan ne aka yi hira da Ismaila Isah Funtua a gidan talabijin na Arise TV. Funtua ya bayyana cewa Ibo ba za su samu mulki a bagas ba har sai sun tsunduma a cikin siyasa.

KU KARANTA: Na yi magan da Funtua kafin ya mutu - Bruce

Yadda Duniya za ta tuna da tsohon Aminin Buhari, Ismaila Isa Funtua
Shugaban kasa, manyan Gwamnati, Bola Tinubu da Isa Funtua a Saudi Hoto: Bashir Ahmaad
Asali: Twitter

Afrilun 2020

Marigayi Isa Funtua ya na cikin wadanda su ka halarci jana’izar Abba Kyari a safiyar 18 ga watan Afrilun 2020. Bayan nan shi da wasu hadiman shugaban kasar sun killace kansu saboda cutar COVID-19.

A wajen jana'izar Dattijon ya bayyana cewa sun yi babban rashi da mutuwar Malam Abba Kyari.

Afrilun 2020

A ranar 21 ga watan Afrilu, 2020, aka yi hira da Marigayi Ismail Funtua a BBC Hausa a game da rade-radin zama sabon shugaban ma’ikatar fadar shugaban kasa. A nan ne Funtua ya ce yafi karfin zama Magajin Abba Kyari a fadar shugaban kasa a tarin shekarunsa.

Yuli 2020

A cikin watan Yuli ne Funtua ya mutu kwastam bayan ya bar gida ya fadawa iyalinsa zai je ganin likita, kafin ya karasa asibiti, 'yanuwansa sun ce ya tsaya a wani shagon aski.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel