NDDC: Akpabio ya yi fallasa, ya bayyana wadanda aka bai wa kwangila

NDDC: Akpabio ya yi fallasa, ya bayyana wadanda aka bai wa kwangila

- Ministan harkokin yankin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya yi zargin cewa 'yan majalisar tarayya sun taka rawar gani wurin rikicin kudi da hukumar ta shiga

- Akpabio ya ce da yawa daga cikin kwangilar da aka fitar a hukumar, duk 'yan majalisar aka bai wa

- Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom ya fuskanci 'yan kwamitin majalisar wakilai domin amsa tambayoyi

Godswill Akpabio, ministan harkokin Neja Delta, ya ce da yawa daga cikin kwangilar da hukumar kula da ci gaban yankin Neja Delta (NDDC) ta fitar duk ta bai wa 'yan majalisar tarayya ne.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa ministan ya yi wannan tsokacin ne yayin da kwamitin majalisar ke tuhumar sa.

Legit.ng ta ruwaito cewa, 'yan majalisar sun kira ministan a ranar Juma'a, 17 ga watan Yuli don kare kan shi a kan badakalar wasu makuden kudade da ake zarginsa da su.

NDDC: Akpabio ya yi fallasa, ya bayyana wadanda aka bai wa kwangila
NDDC: Akpabio ya yi fallasa, ya bayyana wadanda aka bai wa kwangila Hoto: The Guardian
Asali: UGC

A wani bangare kuwa, Legit.ng ta ruwaito cewa kungiyar daliban Najeriya ta yi barazanar fallasa wasu al'amuran rashawa a NDDC.

An gano cewa kungiyar ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tabbatar da cewa ya karbi bayanan kashe kudin hukumar don gudun zagon kasa ga kokarinsa.

A wata takarda da aka mika ga manema labarai a ranar Asabar, 18 ga watan Yuli, Kwamared Danielson Bamidele Akpan, shugaban kungiyar, ya tabbatar da cewa daliban Najeriya za su yi zanga-zanga matukar wani ya yi kokarin hana binciken.

KU KARANTA KUMA: Akeredolu ya yi nasara, ya samu tikitin takara a APC jihar Ondo

A baya mun ji cewa an kara yawan jami'an tsaro a majalisar dattawa a ranar Litinin kafin bayyanar Sanata Godswill Akpabio a gaban kwamitin kula da harkokin Neja Delta na majalisar wakilai.

Kwamitin na bincikar zargin almundahanar wasu kudade da aka ware don habbaka yankin.

Akpabio wanda shine ministan kula da harkokin Neja Delta na fuskantar zargin handame kudade, rashawa, cin zarafi da sauransu daga wurin manajan daraktan NDDC, Joy Nunieh.

Ya musanta dukkan zargin da ake masa.

Nunieh ta bayyana gaban kwamitin majalisar wakilai a ranar Juma'a ta yanar gizo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel