Yanzu Yanzu: An sallami Shugaban NDDC daga asibiti

Yanzu Yanzu: An sallami Shugaban NDDC daga asibiti

- An sallami Farfesa Kemebradikumo Pondei daga asibiti

- A yau ne mukaddashin manajan daraktan na hukumar ci gaban Neja Delta (NDDC) ya fadi ya sume

- Lamarin ya kawo cece-kuce a tsakanin yan Najeriya

An sallami mukaddashin Manajan Darakta na hukumar ci gaban Neja Delta, Farfesa Kemebradikumo Pondei, daga asibiti, Channels Television ta ruwaito.

An tattaro cewa Farfesa Pondei, wanda ya sume a yau Litinin yayinda ya ke amsa tambayoyi a gaban kwamitin majalisar dattawa kan NDDC ya bar asibitin da aka kaishi kimanin sa’a guda da ta gabata.

Kwamitin da ke binciken Pondei ya sanya shi gaba da tambayoyi kusan sama da sa’a guda lokacin da ya bingire tare da sumewa a kan teburin da ke gabansa.

Ana haka, sai wani mutum ya fito ya wage masa baki bayan ya fara bori yayinda sauran mutane suka mikar dashi zaune.

Bayan nan ya gaza samun sukuni don haka aka fitar dashi daga dakin taron.

Yanzu Yanzu: An sallami Shugaban NDDC daga asibiti
Yanzu Yanzu: An sallami Shugaban NDDC daga asibiti Hoto: Channels TV
Asali: Twitter

Kakakin majalisar wakilai, ya sanar da taron bayan fitar da shugaban na NDDC, cewa likitansa da wasu likitoci a majalisar dokokin tarayyar na bashi kulawa.

Da yake magana bayan faruwar lamarin, ministan harkokin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio ya yaba da taimakon da Gbajabiamila ya baiwa Pondei.

Ana sanya ran likita zai saki rahoto a kan lafiyar Pondei domin jama’a su san halin da ake ciki bayan faruwar lamarin da ya janyo cece-kuce tsakanin ‘yan Najeriya.

Yayinda wasu ke ganin dirama ne Shugaban NDDC din ke yi, wasu na fadin a sa kwararrun masana kiwon lafiya su duba shi da kyau.

Wani dan jarida, Dyepkazah Shibayan, ya bayyana cewar dakin kwamitin ya dauki zafi sosai kafin Pondei ya sume.

Kwamitin bincike ya yi zargin cewa Mista Pondei ya kashe kudaden NDDC da yawansu ya kai biliyan N40 ba tare da saka kudin a cikin kasafi ba.

A makon jiya ne kwamitin majalisar ya fara gayyatar tsofin shugabanni da ma su ci yanzu a hukumar NDDC domin amsa tambayoyi a kan badakalar da ake zargin ana tafkawa a hukumar.

Shugaban kwamitin binciken, Tunji - Ojo, ya sanar da yin murabus a ranar Litinin yayin zaman kwamitin domin cigaba da gudanar da binciken badakala a hukumar NDDC.

A ranar Alhamis din makon jiya ne Pondei ya jagoranci mukarrabansa wajen ficewa daga dakin da kwamitin majalisa ke yi ma sa tambayoyi a kan zargin badakala a hukumar NDDC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel