N1.32bn kawai muka rabawa junanmu tallafin Covid-19 ba N1.5bn ba - Shugaban NDDC

N1.32bn kawai muka rabawa junanmu tallafin Covid-19 ba N1.5bn ba - Shugaban NDDC

Mukaddashin shugaban hukumar kula da ci gaban Neja Delta (NDDC), Kemebradikumo Pondei, ya ce hukumar ta kashe naira biliyan 1.32 a matsayin kudin tallafin annobar korona ga ma'aikatanta ba naira biliyan 1.5 da labarai ke ta ruwaitowa ba.

Pondei ya sanar da hakan ne a ranar Litinin yayin da ya gurfana a gaban kwamitin majalisar wakilai a kan zargin su da ake da watanda da wasu makuden kudade.

Ya ce a dangane da tallafin, naira biliyan 1.5 kawai aka yi amfani da shi wurin kula da ma'aikatan duk da cewar an biya su albashinsu.

"An bai wa matasa tallafi don rage radadin da annobar ta zo da shi ga jama'a. Matasan basu da aikin yi kuma don gujewa rikici, an biya su," ya kara da cewa.

"Miliyan biyar na matasa, miliyan biyar na mata sannan miliyan biyar na nakasassu a kowacce mazaba," yace.

Amma kuma da aka sake tambayarsa a ranar Litinin a kan kudin tallafin, ya ce babu mamaki ya fadi naira biliyan 1.5 biliyan ne a lokacin da hankalinsa baya jikinsa.

"Yawan kudin da kwamitin rikon kwarya suka yi amfani da shi ya kai naira biliyan 1.32 ba naira biliyan 1.5 ba," ya bada amsa ga tambayar da kwamitin yayi masa bayan fitar shugaban kwamitin da aka zarga da son kai.

Mun kashe N1.32 biliyan ga ma'aikata a kan tallafin korona - MD na NDDC
Mun kashe N1.32 biliyan ga ma'aikata a kan tallafin korona - MD na NDDC Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Pondei ya musanta zargin da ake musu na cewa suna kara yawan kasafin kudi don kwashe sauran domin amfanin kansu.

Pondei ya kara da cewa, an kashe wata naira biliyan 81.5 daga watan Oktoban 2019 zuwa watan Mayun wannan shekarar.

A karin bayani, ya ce kwamitin rikon kwarya ya kashe naira biliyan 59.1 tun daga hawansu mulki a watan Fabrairu da ta gabata.

"Daga ciki, naira biliyan 38.6 an kashesu ne a kan manyan ayyuka. naira biliyan 35.3 kuwa an kashesu ne a kan 'yan kwangilar da wancan mulkin basu biya ba."

Ya kara da cewa, "an kashe naira biliyan 20.5 a kan ayyukan yau da kullum tsakanin watan Fabrairu 2019 zuwa Mayun wannan shekarar. Akwai kuma bashi da ake bi a shekaru 3 da suka gabata.

"Akwai wasu alawus da aka kwashe shekaru 3 ba a biya ba duk mun biya. Ba a bai wa 'yan makaranta tallafi ba tun 2016, shi ma mun bai wa kowa N500,000."

An tsagaita kadan da sauraron Pondei bayan da kanshi ya fara yin kasa sannan ya fadi a kan teburin gabansa.

A lokacin da ya fara neman shidewa, wasu 'yan majalisar sun bashi taimakon gaggawa.

Daga bisani, an fitar da Pondei inda aka tsagaita na mintuna 30.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng