Buhari ya aikawa Sarki Salman sako na fatan samun sauki

Buhari ya aikawa Sarki Salman sako na fatan samun sauki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, ya aike wa da Sarkin Saudiya, Salman Bin Abdulaziz sakon fatan alheri da kuma samun sauki yayin da aka kwantar da shi a gadon asibiti.

Wannan sako yana kunshe cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya sanya wa hannu kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Shugaban ya ce: "A madadi ni na, gwamnati da jama'ar Najeriya, ina yin addu'ar fatan alheri da kuma samun sauki ga Sarkin Saudiyya, daya daga cikin mafi kyawun shugabannin da na taba haduwa da su a yayin mu'amala da shugabannin duniya."

Sarki Salman
Hoto daga Jaridar Daily Nigerian
Sarki Salman Hoto daga Jaridar Daily Nigerian
Asali: Twitter

"Sarki Salman aboki ne na kwarai wanda ya bai gaza wajen tabbatar da Najeriya a kowane lokaci ta hanyar hadin gwiwa da aiki tare."

"A yayin da Sarkin yake samun kulawa a asibiti, ina masa fatan alheri da addu'o'in samun lafiya cikin gaggawa."

Legit.ng ta ruwaito cewa, Sarki Salman na kasar Saudiya ya na kwance a wani asibiti sakamakon larura da ya samu a mafitsararsa.

Rahotannin da su ke fitowa daga gidajen jaridun kasar a ranar Litinin, sun tabbatar da cewa an kwantar da sarkin mai shekaru 84 a asibiti.

SPA, Kamfanin dillacin labarai na kasar Saudiya ya bayyana cewa an dai kwantar da Salman Bin Abdul'aziz ne a wani asibiti da ke babban birnin Riyadh.

Bayan rahotannin da suka bayyana cewa Sarki Salman ya na fama da kumburi a mafitsararsa, babu wani labari da aka samu game da halin shugaban.

KARANTA KUMA: An kubutar da Almajirai 15 daga wata cibiyar azabtarwa a jihar Neja

Yanzu haka ana yi wa Sarkin na Saudiyya, kuma mai kula da masallatan musulunci masu tsarki da ke biranen Makkah da Madina gwaje-gwaje a asibiti.

Dattijon Sarkin ya yi shekaru biyar ya na mulki, amma ana ganin babban ‘dansa kuma yarima mai jiran gado watau Mohammed Bin Salman ya ke jan ragamar kasar.

Sakamakon rashin lafiyar da ta kama Sarkin, Firayim Ministan kasar Iraki, Mustafa al-Kadhimi, ya dakatar da ziyarar da ya yi niyyar kai wa zuwa kasar Saudi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel