Harkallar NDDC: Tsaro ya tsananta a majalisar tarayya kafin isowar Akpabio

Harkallar NDDC: Tsaro ya tsananta a majalisar tarayya kafin isowar Akpabio

- An tsaurara matakan tsaro a majalisar dattawa a ranar Litinin kafin bayyanar Sanata Godswill Akpabio a gaban kwamitin kula da harkokin Neja Delta na majalisar

- Majalisar dai na bincikar zargin almundahanar wasu kudade da aka ware don habbaka yankin

- Za a fara binciken ne a yau Litinin da karfe 11:00 na safe

An kara yawan jami'an tsaro a majalisar dattawa a ranar Litinin kafin bayyanar Sanata Godswill Akpabio a gaban kwamitin kula da harkokin Neja Delta na majalisar wakilai.

Kwamitin na bincikar zargin almundahanar wasu kudade da aka ware don habbaka yankin.

Akpabio wanda shine ministan kula da harkokin Neja Delta na fuskantar zargin handame kudade, rashawa, cin zarafi da sauransu daga wurin manajan daraktan NDDC, Joy Nunieh.

Ya musanta dukkan zargin da ake masa.

Harkallar NDDC: Tsaro ya tsananta a majalisar tarayya kafin isowar Akpabio
Harkallar NDDC: Tsaro ya tsananta a majalisar tarayya kafin isowar Akpabio Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Nunieh ta bayyana gaban kwamitin majalisar wakilai a ranar Juma'a ta yanar gizo.

Har yanzu ba a san ta yadda Akpabio zai bayyana gaban kwamitin ba.

Kamar yadda gidan talabijin na Channels ya bayyana, kwamitin zai mayar da hankali a kan yadda aka kashe kudaden hukumar kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarta.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: Oshiomhole ya sha alwashin tsige Obaseki daga kujerarsa

Ana sanya ran bayyanar manajan daraktan hukumar, Daniel Pondei a yau a gaban kwamitin.

Za a fara binciken ne a yau Litinin da karfe 11 na safe.

A baya mun ji cewa, Joy Nunieh, tsohuwar mukaddashin manajan daraktar hukumar kula da ci gaban yankin Neja Delta (NDDC), ta zargi Godswill Akpabio, damfara.

Nunieh ta zanta da manema labarai bayan bayyana da tayi a gaban kwamitin wucin-gadi na majalisar dattawa a kan bincikar NDDC.

Akpabio da Nunieh sun gurfana a gaban majalisar ne yayin da ake zargin watanda da N40 biliyan da kwamitin rikon kwarya na NDDC yayi.

A yayin sauraronsu, Akpabio ya ce bai san tsarin ayyukan NDDC ba a zamanin Nunieh saboda ta ki yi mishi bayanin komai.

Amma Nunieh wacce ta jero wasu zarge-zarge a kan Akpabio, ta ce ministan ya tsigeta ne saboda ta ki bashi hadin kai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel