Gwamna Masari ya fasa kwai, ya bayyana masu daukar nauyin 'yan bindiga

Gwamna Masari ya fasa kwai, ya bayyana masu daukar nauyin 'yan bindiga

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya danganta hauhawar miyagun ayyukan 'yan bindiga da gagarar 'yan ta'addan Boko Haram da ke addabar arewa da 'yan siyasa masu son takara a 2023.

Wannan na zuwa ne bayan da 'yan bindiga a jihar Zamfara suka mika bindigogi 50 a makon da ya gabata don amincewa da karbar shanu biyu da gwamnan ya ce zai bada ga duk wanda ya kawo bindiga daya.

Gwamnan ya ce, wadannan 'yan siyasar sun yadda cewa ta hanyar daukar nauyin 'yan bindiga da sauran 'yan ta'adda ne kawai za su iya bata wa mulkin Buhari suna don samun damar mulkar kasar nan a gaba.

Masari, wanda ya yi wannan jawabin a jiya tare da shugabannin guduma da kananan hukumomi na APC, ya ce da yawa daga cikin 'yan bindigar da 'yan Boko Haram da ke kai hari a kasar nan na bin umarnin wasu 'yan siyasa ne.

"Da yawa daga cikin hare-haren 'yan bindiga da Boko Haram da yankin arewaci ke fuskanta, duk wasu 'yan siyasa kuma makiyan gwamnatin APC suke daukar nauyi a matakin tarayya da jiha.

"A zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ana samun tashin bama-bamai a Maiduguri, Kano da Abuja.

Gwamna Masari ya fasa kwai, ya bayyana masu daukar nauyin 'yan bindiga
Gwamna Masari ya fasa kwai, ya bayyana masu daukar nauyin 'yan bindiga. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: WAEC da Najeriya an cimma matsaya, an dage ranar fara jarabawa

"Akwai lokacin da bam ya tashi a Kano inda ya kashe fiye da mutum 500. Masallatai, majami'u da tituna duk an rufesu saboda rashin tsaro. Amma yanzu, Ubangiji ya tsaremu daga irin wannan rashin tsaron amma duk mun manta.

"A yau, 'yan siyasar da ke da burin tsayawa takara ne ke daukar nauyin 'yan bindiga. Daga yadda suka kware a amfani da bindiga da kuma yadda suke kaiwa sojoji hari, za mu gane cewa akwai wata a kasa.

"Suna cewa mun kori PDP saboda rashin tsaro, a don haka ne suke son yin amfani da rashin tsaron don korar APC. Saboda haka ne yakamata mu APC mu bude idanunmu," yace.

Ya yi bayanin cewa dakarun sojin da sauran jami'an tsaro suna matukar kokari wurin ganin bayan ta'addanci. Ya ce babbar matsalar shine yadda sauran masu ruwa da tsaki suka kasa basu tallafi don yakar al'amarin.

Ya ce idan sauran masu ruwa da tsaki za su yi rabin kokarin da dakarun soji ke yi, tabbas Najeriya za ta yi nasarar kawo karshen ta'addanci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel