Boko Haram: Modu Sulum, sabon kwamanda mai matukar hatsari

Boko Haram: Modu Sulum, sabon kwamanda mai matukar hatsari

A makonni kadan da suka gabata, dakarun sojin Najeriya da ke yakar Boko Haram a yankin arewa maso gabas suna fuskantar rashe-rashe sakamakon yadda 'yan ta'addan suka taso da karfinsu.

A kwanaki kadan da suka gabata, mayakan sun kashe sojoji 20 da farar hula 40 a tagwayen harin da suka kai Monguno da Nganzai.

ISWAP sun tabbatar da cewa sune ke da alhakin wannan harin. Wannan na zuwa ne kuwa bayan da hukumar sojin ta tabbatar da ta kai mayakan ta'addancin kasa.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa daya daga cikin kwamandojin da suka shirya wadannan miyagun hare-haren da ke salwantar da rayukan dakarun da farar hula shine babban kwamandan Boko Haram, Modu Sulum.

Waye Modu Sulum?

Bincike ya nuna cewa shine kwamanda mara tausayj da ke jagorancin ayyukan kungiyar a yankin Allagarno da ke karamar hukumar Kaga, da kuma sassan tafkin Chadi. Tsohon mai siyar da itace ne.

Dan asalin Kagan kamar yadda majiyoyi suka tabbatar, yana daukar itace daga kauyen Mainok zuwa garin Maiduguri a baya kafin ya shiga kungiyar Mohammed Yusuf wanda yanzu ta zama Boko Haram.

"Baya yafiya," wata majiya da ta san shi a baya ta sanar.

"Idan ka yi mishi laifi, sai ya dauka fansa. Yana da tsauri da gaggawa," ta kara da cewa

Majiyar ta ce Sulum yana tuka wata motar daukar icce. Yana cikin shekarunsa na arba'in da doriya kuma yana da mata tun kafin ya shiga kungiyar.

Majiyar da ta ce a boye sunanta saboda bata san inda labarin zai kai ba, ta ce sun san Sulum na halartar karatuttukan Mohammed Yusuf kuma sun ja mishi kunne a kan hakan.

"Mun ja mishi kunne a wancan lokacin amma dan gani-kashenin Mohammed Yusuf ne," yace.

A 2009, Mohammed Yusuf ya jagoranci muguwar kungiyar wacce dakarun soji suka murkusheta tare da halaka daruruwan 'yan kungiyar.

Ragowar shugabannin kungiyar ne suka koma ta kasan kasa suka kafu tare da Modu Sulum.

A 2011, kungiyar ta sake tasowa karkashin Abubakar Shekau kuma ta fara harar dakarun soji inda ta kashe dubban jama'a tare da tagayyara tattalin arzikin yankin arewa maso gabas.

A lokacin da kungiyar ta rabu gida biyu, Modu Sulum ya yanke shawarar komawa bangaren ISWAP. A karkashin mulkin dan Yusuf, Abu Mus'ab Albarnawi, sun tare a yankin tafkin Chadi.

Bayan da jama'ar Mamman Nur suka kashe shi sakamakon wani hargitsi a cikin kungiyar, majiyoyi da dama sun ce sauran kwamandojin sun koma karkashin Ba Lawan.

Karkashin wannan shugabancin, Sulum, Modu Borzogo da wani Kannami suka zama shugabannin inda aka bai wa kowanne yankinsa.

Boko Haram: Modu Sulum, sabon kwamanda mai matukar hatsari
Boko Haram: Modu Sulum, sabon kwamanda mai matukar hatsari. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda maza 10 suka yi gwajin 'gwaninta' a kaina - Matashiya mai shekaru 19

A halin yanzu, Sulum ke rike da Talala, sansanin Ajiki Mongusu kuma sauran bangarorin na hada kai da shi wurin kai hare-hare. An gano cewa sun kwace motocin yaki kusan tara daga dakarun soji.

Harinsu na farko a kan rundunar sojin ya samu jagorancin Manjo Ali Almanga ne inda suka kwace makamai masu tarin yawa.

Daily Trust ta gano cewa, Sulum ne ya jagoranci harin kauyen Felo da ke Gubio inda aka kashe farar hula 81 a watanni kadan da suka gabata.

Wannan kuwa ya sha banban da tsarin ISWAP inda suke barin farar hula matukar sun kai hari.

Wannan yanayin tsarin harin ne aka fuskanta a Nganzai inda aka halaka farar hula masu tarin yawa.

Bangaren Sulum ake zargi da harin Monguno, ofishin 'yan sanda da kuma sojoji.

Majiyoyin sun kara da cewa akwai yuwuwar shine ya shirya harbo jirgin majalisar dinkin duniya a Damasak.

"Muna lura da yanayin ayyukansu kuma muna zargin bangaren Modu Sulum sun fi matukar hatsari a cikin bangarorin ISWAP," yace.

A yayin da bangaren Sulum suke ta kai hari, bangaren Shekau sun yi shiru kamar yadda majiyar tace. Masu kiyasi sun ce wannan barnar babbar barazana ce ga nasarorin da dakarun soji ke samu.

"Mutane na matukar tsoron Amir Modu Sulum. An san shi da amfani da layu da sihiri. Babban shaidanin kwamanda ne," majiyar ta kara da cewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel