Da duminsa: Hukumar Sojin Sama ta bayyana ranar Jana'izar Tolulope Arotile (Hotuna)

Da duminsa: Hukumar Sojin Sama ta bayyana ranar Jana'izar Tolulope Arotile (Hotuna)

Hukumar mayakan saman Najeriya NAF ta bayyana cewa za'a yi jana'izar matukiyar jirgi mai saukar angulu ta farko a tarihin Najeriya, Tolulope Arotile ranar Alhamis, 23 ga Yuli, 2020.

Za'a birneta ne a makabartar hafsoshin Sojin Najeriya dake unguwar Karmajiji, birnin tarayya Abuja.

Hukumar ta bayyana hakan ne yayinda ministar harkokin mata, Pauline Tallen; ministan labarai, Lai Mohammed, da mambonin majalisar dattawa suka kai gaisuwar ta'aziyya.

A jawabin da kakakin hukumar, Ibikunle Daramola, da ya saki a shafin Tuwita, ya bayyana cewa za'a birneta cikin kwalliya na musamman da ake yiwa manyan hafsoshi.

Jawabin yace: "Za'a yi jana'izar marigayiya, Tolulope Arotile, matukiyar jirgi mai saukar angulu ta farko a tarihin Najeriya, wacce ta mutu ranar 14 ga Yuli, 2020 a ranar 23 ga Yuli 2020 a makabartar Sojin tarayya dake Abuja."

"Hakazalika babban hafsan Sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar, ya karbi bakuncin wasu mambobin majalisar shugaban kasa da wasu mambobin majalisar dattawa da suka kawo masa ziyara da Hedkwatar NAF ranar Alhamis domin mika gaisuwar ta'aziyya."

"Daga cikinsu akwai Ministar harkokin mata, Dame Tallen Pauline da kuma Ministan Labarai da al'adi, Alhaji Lai Mohammed."

"Hakalika akwai tawagar mambobin majalisar dokokin tarayya kimanin mutane 20 karkshin jagorancin shugaban kwamitin hukumar Soji a majalisar dattawa, Sanata Bala Ibn-Na'Allah.

Kalli hotunan ziyarar:

Da duminsa: Hukumar Sojin Sama ta bayyana ranar Jana'izar Tolulope Arotile (Hotuna)
Da duminsa: Hukumar Sojin Sama ta bayyana ranar Jana'izar Tolulope Arotile (Hotuna)
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yan Najeriya 70,000 daga Sokoto da Katsina sun tsere zuwa Nijar

Da duminsa: Hukumar Sojin Sama ta bayyana ranar Jana'izar Tolulope Arotile (Hotuna)
Da duminsa: Hukumar Sojin Sama ta bayyana ranar Jana'izar Tolulope Arotile (Hotuna)
Asali: Twitter

Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta sanar da mutuwar matukiyar jirgin yakinta mace ta farko, Tolulope Arotile, wacce ta mutu watanni takwas bayan kammala karatunta da yayeta.

NAF ce ta sanar da labarin mutuwar Arotile, wanda aka bayyana a matsayin abun “takaici” a cikin wani jawabi a ranar Talata, 14 ga watan Yuli.

An tattaro cewa marigayiyar sojar ta rasu ne sakamakon bugunta da mota da wani abokinta yayi a sansanin sojin sama (NAF Base) a Kaduna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel