A zuwa Z din kudirin da ‘Yan Majalisa su ka kawo domin hana lalata da ‘Yan makaranta

A zuwa Z din kudirin da ‘Yan Majalisa su ka kawo domin hana lalata da ‘Yan makaranta

Sanatoci su na yunkurin kawo wani kudiri wanda idan ya zama doka ake sa ran za a ga raguwar barna da ake yi a manyan makarantun Najeriya.

Mun tsakuro maku wasu kadan daga cikin sassan wannan kudiri kamar yadda Punch ta kawo:

Duk wanda ya aikata wadannan zai fada sahun wadanda su ka yi barazanar yin lalata:

Za a kama:

A. Duk Malamin da ya kwanta ko nemi ya kwanta da ‘dalibi(a) ko mai neman shiga makaranta.

B. Duk Malamin da ya yi wa ‘dalibi(a) barazana ko ya jefa shi/ita cikin wani hali ta hanyar neman yin lalata ko kuma;

C. Ya jefa wani/wata ya/ta yi lalata ko ya/ta;

D. Rungume, sumbanci, tab'a, tsikara, ko shafa gaba ko mama ko wani bangaren jikin ‘dalibi(a)

E. Ya yi amfani da hannunsa ya aikawa ‘dalibi(a) bidiyo ko wani abu da ya kunshi hotuna ko bidiyon tsiraici.

F. Ya yi fito, ko kifta idanuwa ko kuma ya yi ihu, ko ya kai ga yin ba’ar lalata ko yi wa halittar ‘dalibi(a) shakiyanci.

KU KARANTA: Fasto ya shiga hannun hukuma da laifin aikata fyade

A zuwa Z din kudirin da ‘Yan Majalisa su ka kawo domin hana lalata da ‘Yan makaranta
Shugaban Majalisa Ahmad Lawan Hoto: NASS
Asali: Facebook

Wannan kudiri har wa yau ya ce:

G. Dalibi/Daliba ba zai iya bada dama ga malami/malama ya yi amfani da shi/ita ba.

H. Za a dakatar da Dalibi/Dalibar da ya/ta yi wa malami/malama sharri.

I. Jami’an makarantar da su ka boye labarin lalata za su fuskanci tarar N5, 000, 000 ko zaman gidan yari ko kuma duka.

J. Dole shugaban makaranta ya kare masu karatu daga barazanar malamai ko ma’aikata daga cikin makaranta ko waje.

Wannan kudiri ya na shan suka da yabo daga jama’a a halin yanzu. Wasu su na ganin cewa ana harin malaman makarantu ne, yayin da ake ta’asa a wasu wuraren aikin.

Kwanakin baya kungiyar ASUU ta bakin shugabanta na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi ta bayyana cewa malaman jami’a ne Sanatoci su ke hari da wannan kudiri.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel