Bidiyon tsoho mai shekara 95 da bai taba yin aski ba tunda ya zo duniya
Doddapalliah, wani tsoho mai shekaru 95 dan kasar Indiya, ya nuna gashin kansa mai tsayin taku 24, wanda ya yi ikirarin cewa bai taba askeshi ba a rayuwarsa.
Saboda tsabagen tsawon gashinsa, sai gammo yake yi da shi ya barshi a kansa, tamkar wanda ya dora kwarya.
Jama'a da dama sun tara gashi a fuskokinsu da kansu sakamakon dokar kulle da aka saka a kasashe daban - daban a fadin duniya.
A yayin da irin wadannan jama'a ke jin cewa sun tara suma da yawa, kuma akwai bukatar su yi aski, shi Doddapalliah bai taba aski ba a iya rayuwarsa da zai iya tunawa.
Yanzu haka jama'a da dama a garin Molakalmuru da ke gundunar Chitradurga suna bawa Doddapalliah wata daraja kwatankwacin ta abin bauta saboda yawan gashin kansa.
Duk lokacin da Daddapalliah zai fita sai an yi aikin tufke gashin kansa; mai tsawon mita 7.3, tare da saka tufafi a daddaure kafin ya iya samun sukunin motsawa cikin kwanciyar hankali.
A wani faifan bidiyo da ya yi farin jini a shafin Newsflare, Doddapalliah da kansa ya nuna cewa ya na da wata nagarta ta ababen bauta kuma a saboda hakan ne ya sa ko sau daya bai taba koda rage yawan sumarsa ba.
Kalli faifan bidiyon tsohon a nan:
Sai dai, da yawan jama'a basu ga wani azancin Daddapalliah na barin wannan uban gashi haka ba a shekarunsa, saboda alamu sun nuna cewa wahalar da shi kawai gashin ya ke, ba kuma wata baiwa ba ce kamar yadda ya ke tunani.
DUBA WANNAN: 'Yanta mayakan Boko Haram 602: Sai da mu ka rantsar dasu kafin sakinsu - DHQ
Ma su wannan ra'ayi suna ganin cewa zai fi sauki ga dattijo Doddapaliah ya aske gashin kansa ya huta, a maimakon ya ke yawan damun mutane su taimaka su daure ma sa gashin duk lokacin da ya fara warwarewa idan ya na tafiya.
A cikin faifan bidiyon, Doddapaliah ya nuna alamun cewa yana jin zafi a yayin da wasu mutane ke kokarin gyara ma sa gashin kansa kafin su dauki hoto.
Ba iya tsayi gashin Doddapalliah ya ke da shi ba, irin kauri da kibar da gashin keda shi wata alama ce da ke nunawa cewa ba a tsaftace shi.
Ba Doddapalliah ne mutum na farko da ya fara shiga kundin tarihi na duniya ba saboda tara yawan gashi.
Sakal Dev Tuddu wani mutum ne a kasar Indiya da ya taba shafe shekaru 40 bai yi aski ba da wani Savjibhai Rathwa; mutumin da ke tattare gashinsa mai tsawon mita 19 tare da nade shi a kafadarsa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng