Zaben Ondo: APC ta nada Gwamna Bello shugaban kwamitin zaben fidda gwani

Zaben Ondo: APC ta nada Gwamna Bello shugaban kwamitin zaben fidda gwani

Jam'iyya mai ta APC, ta zabi gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, a matsayin wanda zai jagoranci kwamitin zaben fidda gwanin takara na gwamnan jihar Ondo.

Gwamna Bello shi ne zai jagoranci kwamitin mutum a yayin zaben fidda gwanin takarar gwamnan Ondo na jam'iyyar APC da za a gudanar a ranar Litinin, 20 ga watan Yuli.

Kwamitin riko na jam'iyyar APC na kasa, ya kuma zabi Emperor Chris Baywood Ibe, ya jagorancin kwamitin mutum 9 da za su daukaka kara kan zaben.

Hakan yana kunshe cikin sanarwar da mataimakin mai magana da yawun jam'iyyar na kasa, Yekini Nabena ya fitar a ranar Alhamis cikin birnin Abuja.

Mista Nabena ya ce wannan nade-nade sun biyo bayan amincewar da shugaban kwamitin riko na jam'iyyar na kasa, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bayar.

Gwamna Yahaya Bello
Hoto daga; Pulse.ng
Gwamna Yahaya Bello Hoto daga; Pulse.ng
Asali: Facebook

'Yan kwamitin zaben fidda gwanin takarar sun hadar da; Olorogun o’tega Emerhor, Alwan Hassan, Chief Samuel Sambo, Hajiya Binta Salihu, Mr. Emma Andy, Dr. Adebayo Adelabu, Abdullahi Aliyu da kuma Mrs. Margret Ngozi Igwe.

Kwamitin daukaka karar sun hadar da; Abdulmimuni Okara, Mr. Festus Fientes, Mr. Okon Owoefiak, Mr. Abba Isah, Alh. Umar Duhu, Hon. Sani El-katuzu, Mrs. Osuere Eunice da kuma Emeka Agaba.

Nabena ya kara da cewa, a ranar Juma'a, 17 ga watan Yuli, Mai Mala zai rantsar da dukkanin 'yan kwamitin a babbar hedikwatar jam'iyyar da ke birnin Abuja.

KARANTA KUMA: Mutum 6 za su maimaita hidimar kasa a Kano - NYSC

Gwamnonin APC da aka dorawa nauyin yakin neman zaben gwamnan jihar Edo, sun gudanar da muhimmin taro domin tattauna hanyoyin da zasu bi domin cimma burinsu a zaben da za a yi a ranar 10 ga watan Satumba.

Legit.ng ta ruwaito cewa, gwamnonin sun gudanar da taron ne a wani wuri da ba a bayyana ba kamar yadda wata majiya a hedikwatar gwamnonin jam'iyyar da ke Abuja ta tabbatar.

Daga cikin kusoshin jamiyyar da suka halarci taron sun hadar da; shugaban kwamitin, gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma, da mataimakinsa Ovie Omo-Agege; da Farfesa Julius Ihonvibere da sauransu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng