Matawalle ga yan bindiga: Ajiye bindiga daya mu baka shanaye biyu

Matawalle ga yan bindiga: Ajiye bindiga daya mu baka shanaye biyu

Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya ce gwamnatinsa ta shirya bada shanaye biyu da duk bindigar AK47 da kowani dan bindiga ya ajiye a jihar, Rahoton Daily Trust.

Matawalle ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayinda ya karbi bakuncin manyan jagororin tsaro da shugaba Muhammadu Buhari ya tura tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso yamma.

Sune Sifeto Janar na hukumar yan sanda, IG Mohammed Adamu, Dirakta Janar na hukumar tsaron farin kaya, Yusuf Bichi, da sauran su.

A cewarsa, "Ga duk makamin da tubabben dan bindiga ya ajiye, za a maye masa da shanaye biyu."

"Ba mu son basu kudi, saboda kada suyi amfani da shi wajen sayen sabbin makamai."

"Mun ce zamu saka musu da shanaye, yan Fulani ne kuma suna bukatar shanaye domin jin dadin arziki."

"Hakazalika mun fadawa yan bindiga su wargaza dukkan wano daba da suke da shi a cikin daji. Ba zamu lamunci yan bindigan da aka amshi makamansu su koma cikin daji zama ba."

"Mun ce su zaba cikin dawowa cikin gari cikin jama'a ko a basu dukiya su zauna inda suke domin fara sabon rayuwa."

"Yawancinsu suna zama ne cikin daji karkashin bishiyoyi da bukka. Shi yasa muka kirkiro shirin RUGA domin taimaka musu."

Matawalle ga yan bindiga: Ajiye bindiga daya mu baka shanaye biyu
Matawalle ga yan bindiga: Ajiye bindiga daya mu baka shanaye biyu
Asali: UGC

KU KARANTA: Rashin jituwa a majalisar dokokin jihar Neja, an tsige shugaban masu rinjaye da mataimakinsa

Gwamna Matawalle ya kara da cewa jihar Zamfara ce cibiyar yan bindiga a Najeriya kuma idan jami'an tsaro zasu iya dakilesu a jihar, sauran sassan yakin arewa maso yamma zasu huta.

Yace: "Dalilin da yasa na fadi haka shine dukkan shugabannin yan bindigan na jihar Zamfara."

"Muna bukatar hukumomin tsaro suyi shiri na musamman."

"Ya kamata a samu hadin kai tsakanin hukumomin tsaro saboda lokacin da aka kai musu hari a Katsina, jihar Zamfara, Sokoto da Kebbi suke guduwa."

IGP Adamu a jawabinsa, ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya umurcesu su kawo karshen lamarin tsaro a kasar saboda hakan na daminsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel