MAKIA: Ban ci zarafin ma'aikacin tashar jirgin sama ba - Abdul'aziz Yari

MAKIA: Ban ci zarafin ma'aikacin tashar jirgin sama ba - Abdul'aziz Yari

- Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari, ya karyata zargin cewar ya ci zarafin wani ma'aikacin tashar jiragen sama na Mallam Aminu Kano

- Haka zalika ya shaidawa Ministan sufurin jiragen sama, Fani-Kayode, da ya jira shammaci daga kotu

- A ranar Laraba, 15 ga watan Yulin 2020, hukumar FAAN ta zargi tsohon gwamnan da ci zarafin ma'aikacin tashar jiragen da karya matakan kariya daga Coronavirus

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari, ya karyata rahotannin da ke yawo na cewar ya ci zarafin wani ma'aikacin tashar jiragen sama a ranar Asabar, a tashar sauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano (MAKIA), Kano.

Haka zalika, Yari ya bayyana cewar ya zama wajibi hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta kasa FAAN, ta janye maganganun da tayi a shafinta na Twitter kan cewar ya karya ka'idoji, da kuma rubuta wasikar ban hakuri akan sharrin da tayi masa.

Yari a cikin wata sanarwa daga mai bashi shawara kan kafofin watsa labarai, Mayowa Oluwabiyi, ya ce duk da cewa yayi amfani da tashar jirgin a wannan rana, amma abunda ake zarginsa da shi bai aikata ba.

Idan za a iya tunawa a ranar Laraba hukumar FAAN a shafinta na Twitter ta wallafa cewa bijirewa matakan kariya na COVID-19 da Yari ya yi abun Allah wadai ne.

KARANTA WANNAN: WASSCE: A shirye muke mu bude makarantu - Jihohin Kudu maso Yamma

MAKIA: Ban ci zarafin ma'aikacin tashar jirgin sama ba - Abdul'aziz Yari
MAKIA: Ban ci zarafin ma'aikacin tashar jirgin sama ba - Abdul'aziz Yari
Asali: Twitter

FAAN ta kara zargin Yari da kin bin matakan da hukumar ta shimfida ta hannun kwamitin dakile yaduwar cutar Coronavirus, inda ya tunkude wani jami'in sashen muhalli, a lokacin da yace lallai sai an sanyawa kayan da Yari yake dauke da su magani.

Amma Oluwabiyu yace: "An nusar da Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara kan labarin da hukumar FAAN ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Laraba, 15 ga watan Yulin 2020, cewar hukumar na zargin tsohon gwamnan ya ci zarafin ma'aikacin tashar jiragen sama ta Mallam Aminu Kano (MAKIA).

"A nan, muna sanar da al'umma cewa H.E Abdulaziz Yari ya bi ta tashar jiragen MAKIA a wannan rana, amma bai ci zarafin ma'aikacin tashar ba. Ya kuma bi duk wasu matakai na kariya daga cutar Covid-19 kamar yadda ita FAAN ta shimfida.

"Lamarin da hukumar ta wallafa a shafin nata sam bai faru ba.

"H.E Abdulaziz Yari ya kalli wannan labari a matsayin batanci da karya tsagoronta, a don haka ya bukaci hukumar FAAN ta janye wannan rubutu, ta kuma gaggauta bashi hakuri akan batancin suna da suka yi akansa."

Yari ya kuma yi nuni da cewa ba zai lamunci yadda Ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode yake cin zarafinsa a shafinsa na Twitter ba, tun bayan da hukumar FAAN ta wallafa wancan labarin.

Yari ya tabbatar da cewa shi ya kasance d'an Nigeria mai bin doka da oda, wanda kuma bai taba cusa kansa a cikin wani aiki na laifi ba.

"H.E Yari ya kasance mai goyon bayan gwamnatin tarayyar Nigeria akan dukkanin matakan da take dauka a yakin da take yi don dakile yaduwar cutar Coronavirus a Nigeria.

"Don haka, martaba da mutuncin Abdulaziz Yari ba zai taba zama abun ayi fatali da shi ba," a cewar Oluwabiyi.

Yari ya kuma ce Fani-Kayode ya saurari shammaci daga kotu, domin kuwa ba zai bar cin mutuncinsa ya tafi a banza ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel