Da dumisa: Shugaban NDDC ya fice daga zauren majalisar tarayya ransa a bace

Da dumisa: Shugaban NDDC ya fice daga zauren majalisar tarayya ransa a bace

- Farfesa Kemebradikumo Pondei, shugaban kwamitin rikon kwarya na NDDC da tawagarsa a ranar Alhamis, sun fice sun bai wa 'yan majalisar wakilai wuri

- Pondei ya ce shi da tawagarsa basu shirya yin wani bayani a gaban kwamitin ba

- Ya ce lallai Olubunmi Tunji-Ojo ba zai iya shugabantar bincike a kan al'amarin da ake zarginsa ba

Mukaddashin manajan daraktan kwamitin rikon kwarya na hukumar kula da harkokin Neja Delta, Farfesa Kemebradikumo Pondei da tawagarsa a ranar Alhamis, sun fice sun bai wa 'yan kwamitin NDDC na majalisar wakilai wuri.

Ya ce shi da tawagarsa basu shirya yin wani bayani a gaban kwamitin ba.

Da dumisa: Shugaban NDDC ya fice daga zauren majalisar tarayya ransa a bace
Da dumisa: Shugaban NDDC ya fice daga zauren majalisar tarayya ransa a bace Hoto: The Nation
Asali: UGC

Pondei ya kaskanta shugaban kwamitin majalisar da ke binciken, Olubunmi Tunji-Ojo, inda ya jaddada cewa ba zai iya shugabantar bincike a kan al'amarin da ake zarginsa ba.

'Yan kwamitin da suka hada da Benjamin Kali, Ben Ibakpa da Shehu Koko, sun sanar da mukaddashin manajan daraktan cewa tunda babu wata takarda a gabansu, a hukumance dole ne ya amsa musu tambayoyinsu.

A yayin da sauran mambobin kwamitin ke bada tasu gudumawar, mukaddashin manajan daraktan ya bukaci barin gaban kwamitin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: FG ta kafa kwamitin bincike a kan NSITF

Amma kafin su amsa ko su hana, ya yi ficewarsa.

Fusatattun 'yan kwamitin sun zargi kwamitin rikon kwarya da kokarin fusata 'yan majalisar tare da mika bukatar a damko shi.

A wani labarin kuma, jami'an 'yan sandan Najeriya sun tsinkayi gidan Joy Nunieh, tsohuwar mukaddashin manajan daraktan hukumar NDDC, inda suka yi masa zobe.

Jami'an tsaron sun isa gidan ne da ke lamba 3, titin Owuru Creek, kusa da titin Herbert Macauley da ke tsohuwar GRA a Fatakwal, jihar Ribas a sa'o'in farko na ranar Alhamis.

Wannan ci gaba ya faru ne kafin isar Nunieh gaban kwamitin bincike na majalisar dattawa da ke Abuja inda za ta amsa tambayoyi a kan ayyukan NDDC.

A yayin da jaridar The Cable ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ribas, Omoni Nnamdi don tsokaci, ya bukaci a kira sa nan da mintuna 30.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng