Gwamna Ganduje ya sauya fasalin majalisar zartarwa ta Kano

Gwamna Ganduje ya sauya fasalin majalisar zartarwa ta Kano

A ranar Laraba, 15 ga watan Yuli, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sauya fasalin majalisar zartarwa ta gwamnatinsa bayan sauya ma'aikatun wasu kwamishinoninsa uku.

Hakan yana kunshe cikin wata sanarwa da babban sakataren sadarwa na fadar gwamnatin Kano, Abba Anwar ya fitar yayin ganawa da manema labarai.

A zaman majalisar da aka gudanar a fadar gwamnatin Kano, Ganduje ya rantsar da sabon kwamishina, Idris Garba Unguwar Rimi, wanda zai kasance ɗaya daga cikin 'yan majalisar zartarwa na gwamnatin jihar.

Gwamna Ganduje yayin zaman majalisar zartarwa na gwamnatinsa da aka gudanar a ranar Laraba, 15 ga watan Yulin 2020
Hoto daga fadar gwamnatin Kano
Gwamna Ganduje yayin zaman majalisar zartarwa na gwamnatinsa da aka gudanar a ranar Laraba, 15 ga watan Yulin 2020 Hoto daga fadar gwamnatin Kano
Asali: Twitter

Hadimin gwamnan ya ce wannan sabon naɗi ya biyo bayan gibin da aka samu a majalisar zartarwa ta gwamnatin bayan tsige wani kwamishina da aka yi a kwanakin baya.

Watanni biyu da suka gabata ne Gwamna Ganduje ya tube kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Injiniya Mu'azu Magaji Dan Sarauniya.

Ganduje ya tsige Dan Sarauniya daga mukaminsa, sakamakon murnar da yayi a kan mutuwar Abba Kyari, tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

KARANTA KUMA: An yankewa wani baƙar fata hukuncin ɗauri na shekaru 48 bayan wata mata ta yi mummunan mafarki a kansa

Mallam Anwar ya ce naɗin sabon kwamishinan da Ganduje shi ne ya janyo sauye-sauye a ma'aikatun wasu kwamishinoni kuma a nan gaba wani sauyin zai sake biyo baya.

Jerin sauye-sauyen da Ganduje ya yiwa majalisar sun hadar:

"Mahmud Muhammad Dansantsi ya tashi daga ma'aikatar kasuwanci zuwa ma'aikatar gidaje da sufuri."

"Barrister M.A. Lawan na ma'aikatar gidaje da sufuri ya koma ma'aikatar shari'a."

"Barrister Ibrahim Mukhtar na ma'aikatar shari'a zuwa ma'aikatar kasuwanci."

Sabon kwamishinan Idris Garba, zai maye gurbin Dan Sarauniya da aka tube a ma'aikatar ayyuka da gine-gine.

Ganduje ya umarci kwamishinonin da su ci gaba da lura da ka'idojin dakile yaduwar cutar korona kamar yadda mahukuntan lafiya suka ambata.

Ya ce "su tabbatar sun kiyaye dokar bayar da tazara, wanke hannu da sabulu a karkashin ruwa mai gudana ko kuma da sunadirin tsaftace hannu (sanitizer) a wurin aiki da kuma gidajensu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel