Masu garkuwa a Kaduna na neman fansar N900m

Masu garkuwa a Kaduna na neman fansar N900m

Masu ta'adar garkuwa da suka yi awon gaba da akalla mutum 20 a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, sun nemi kudin fansa na Naira miliyan 900 kafin su sako mutanen da suka yashe.

Biyo bayan wannan mummunan hari da 'yan bindiga suka kai ranar Lahadi, ya kuma janyo salwatar rayukan mutane biyu da suka kashe a garin Keke na karamar Hukumar Chikun ta jihar.

Rahotanni daga jaridar Daily Trust sun bayyana cewa, maharan sun kuma nemi kudin fansa har ta naira miliyan 900 gabanin sakin akalla mutum 20 da suka yi awon gaba da su.

Mazauna garin Keke sun bayar da shaidar cewa, maharan sun yi basaja cikin kakin dakarun soji da na jami'an 'yan sanda, inda suka sanya wani shinge a kan wata hanyar a daren Lahadi.

Babban Sufeton 'Yan sandan Najeriya; Muhammad Adamu
Babban Sufeton 'Yan sandan Najeriya; Muhammad Adamu
Asali: Facebook

'Yan uwan wata mai abincin sayarwa 'yar shekara 19 da 'yan bindigar suka yi garkuwa da ita sun ce masu ta'adar sun yi barazanar mayar da ita farkarsu muddin ba a ba su kudin fansa na naira miliyan 200 ba a kanta.

Wani kawun budurwar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaidawa manema labarai cewa, "masu garkuwar sun yi awon gaba da 'yar tasa yayin da take kan hanyar komawa gida da misalin karfe 8.30 na dare."

KARANTA KUMA: Yadda 'yan bindiga suka kashe hakimi a Kebbi

"Masu garkuwar sun kira mu a ranar Litinin da Yamma suna neman kudin fansa na naira miliyan 200. Sun kuma sake kira a ranar Talata da rana domin jin ko kudin sun samu."

"Mahaifinta direban baburin A daidaita sahu ne kuma babur din ma ba na shi ba ne."

"Sun yi barazanar cewa idan har muka kasa biyan kudin fansar za su mayar da ita tamkar matar su," in ji shi.

Sai dai har ya zuwa lokacin da aka tattaro wannan rahoto, manema labarai ba su samu nasarar jin ta bakin kwamishinan harkokin tsaron cikin gida ba na jihar Kaduna, Samuel Aruwa.

Haka zalika Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Mohammed Jagile bai dauki kiran da aka rika rangada masa ba ta wayar salula.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel