Sojoji sun kashe 'yan bindiga 6, sun bankado shirin satar dabbobi a Zamfara da Katsina

Sojoji sun kashe 'yan bindiga 6, sun bankado shirin satar dabbobi a Zamfara da Katsina

Hedkwatar tsaro ta ce dakarun atisayen Sahel Sanity sun kashe 'yan bindiga shida tare da bankado wani yunkurin satar dabbobi a jihohin Katsina da Zamfara a tsakanin ranar 13 da 14 ga watan Yuli.

Shugaban fannin yada labarai, John Enenche, a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba, ya ce an samu wannan nasarar ne a ranar 14 ga watan Yuli bayan bin rahoton sirri da suka yi.

Manjo Janar Enenche, ya ce dakarun sun samu taimakon helikoftan yaki na rundunar Operation Hadarin Daji, wadanda suka tsinkayi 'yan bindigar da ke tsaunikan Komai da ke dajin Rukudawa na yankin jihar.

Ya kara da cewa, dakarun sun rinjayi karfin 'yan bindigar inda suka kashe shida daga ciki yayin da sauran suka tsere da raunikan harbin bindiga.

Kamar yadda yace, an samu bindiga daya kirar AK 47, harsasai da babura 34.

Shugaban fannin yada labarai ya kara da cewa, a ranar 13 ga watan Yulin 2020, dakarun sun samu kiran gaggawa a kan cewa 'yan bindiga sun yi yunkurin shiga kauyen Kasele da ke karamar hukumar Batsari don satar Shanu.

Sojoji sun kashe 'yan bindiga 6, sun bankado shirin satar dabbobi a Zamfara da Katsina
Sojoji sun kashe 'yan bindiga 6, sun bankado shirin satar dabbobi a Zamfara da Katsina. Hoto daga Premium Times
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An bi mamallakin kamfani GoKada an kashe har gida

Ya ce a yayin da dakarun suka gaggauta isa kauyen, 'yan bindigar sun watse inda suka bar dabbobin.

Kamar yadda yace, zakakuran sojojin sun ci gaba da zama a kauyen har sai da kwanciyar hankali ya dawo.

"Shugabannin hukumar tsaro na taya zakakuran sojojin murna a kan wannan kokarin tare da basu kwarin guiwar ci gaba da yakar ta'addanci a yankin," yace.

A wani labari na daban, masu ta'adar garkuwa da suka yi awon gaba da akalla mutum 20 a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, sun nemi kudin fansa na Naira miliyan 900 kafin su sako mutanen da suka yashe.

Biyo bayan wannan mummunan hari da 'yan bindiga suka kai ranar Lahadi, ya kuma janyo salwatar rayukan mutane biyu da suka kashe a garin Keke na karamar Hukumar Chikun ta jihar.

Rahotanni daga jaridar Daily Trust sun bayyana cewa, maharan sun kuma nemi kudin fansa har ta naira miliyan 900 gabanin sakin akalla mutum 20 da suka yi awon gaba da su.

Mazauna garin Keke sun bayar da shaidar cewa, maharan sun yi basaja cikin kakin dakarun soji da na jami'an 'yan sanda, inda suka sanya wani shinge a kan wata hanyar a daren Lahadi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel