Zargin lalata: Ministan Buhari ya yi martani

Zargin lalata: Ministan Buhari ya yi martani

A ranar Litinin, ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio ya ki yin martani ga tsohuwar manajan daraktar kwamitin NDDC, Joy Nunieh, wacce ta zargesa da yunkurin lalata da ita.

Nunieh ta yi magana a wani shirin Arise TV bayan da ministan ya musanta zargin damfara da ake masa.

Ta ce rashin shigarta cikin miyagun ayyukansa ne yasa ya sallameta.

A martaninsa, Akpabio ya ce tana da matsalar halayya kuma ya yi ikirarin hakan ne yasa aurenta suka dinga mutuwa.

A yayin jawabi a ranar Litinin, Nunieh ta ce ministan ya bijiro mata da bukatarsa ta lalata tare da yi mata alkawarin zai tabbatar da ita a matsayin shugabar NDDC.

Zargin lalata: Ministan Buhari ya yi martani
Zargin lalata: Ministan Buhari ya yi martani Hoto: Vanguard
Asali: UGC

"Na mareshi a lokacin da yayi kokarin lalata da ni," Nunieh ta yi zargi.

Amma kuma, a lokacin da aka fuskanci ministan a ranar Talata da wannan zargin, ya ki yin tsokaci a kai.

"Kada mu mayar da hankali a kan wasu abubuwa na daban. A wurina, habbaka yankin Neja Delta ne abinda ke daukar hankalina.

"A matsayina na minista a kasar nan, ba zan iya magana a kan wani mutum ba. Zan iya zantawa ne a kan abinda zai kawo ci gaba. Abububwa da za su kawo habbaka kuma masu amfani ga gwamnatin tarayya," yace.

A yayin da aka tambayeshi ko me zai iya cewa a kan zargin yunkurin lalata da Joy Nunieh da tayi ikirarin yayi, sai yace "maganar habbaka yankin Neja Delta ake da kuma yadda za a kawo ci gaba ga jama'ar.

"Dole ne a mayar da hankali a kan abubuwan da suka dace don sune suke daukar hankalina.

"Akwai bukatar mu san cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu nasarori masu tarin yawa a bangaren ci gaban ababen more rayuwa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Matukiyar jirgin yakin Najeriya mace ta farko ta rasu

"Tun da na zama dan siyasa har na kai matakin kwamishina a jihar Akwa Ibom na tsawon shekaru 6. Na yi gwamnan jihar na tsawon shekaru 8. Na yi shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa yanzu ga ni a matsayin minista.

"Duk inda naje ina kokarin ganin na bar wani abun ci gaba. Hakan yasa nake kokarin ganin burin shugaban kasa ya cika tare da cika alkawurran da yayi a yayin neman zabe," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel