Hukuma ta kama wata Mata da ke aiki a NNPC ta na azabtar da boyi-boyinta

Hukuma ta kama wata Mata da ke aiki a NNPC ta na azabtar da boyi-boyinta

An kama wata ma’aikaciya da ke aiki da kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC, a Kaduna, Yemi Awolola, bisa zargin lalata da azabtar da ‘yar aikinta.

Misis Yemi Awolola ta azabtar da wannan yarinya ‘yar shekara 14 da ke yi mata aikace-aikace a gida.

Jaridar Daily Trust ta ce matar ta dauko wannan yarinya ne daga sansanin ‘yan gudun hijira da ke karamar hukumar Kajuru, kusan shekara daya da rabi da ya wuce.

Awolola ta dauki yarinyar ne daga hannun iyayenta da sunan cewa za ta sa ta makaranta, yayin da ita kuma za ta rika taimaka mata da aikace-aikacen gida.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan mata da iyalinta sun rika tsirawa yarinyar na’urar kyatsa wuta a cikin mafitsara, sannan kuma an babbake mata sashen jikin na ta.

Misis Awolala ta yi amfani da wannan na’ura ta kyasta wuta wajen kona mafitsarar yarinyar.

KU KARANTA:

Hukuma ta kama wata Mata da ke aiki a NNPC ta na azabtar da boyi-boyinta
Hafsah Baba Hoto: Twitter
Asali: Twitter

Kwamishinar harkokin jama’a da walwala ta jihar Kaduna, Hafsat Mohammed Baba, ta ce a wasu lokutan, a kan bar wannan yarinya ta na kwana a cikin ban-daki.

Bayan haka kuma a kan ba wannan yarinya ruwan sha daga ban-dakin. Kwamishinar ta ce wannan mugun aiki ya sabawa dokokin kare hakkin yara a jihar Kaduna.

Hafsat Baba ta kuma shaidawa ‘yan jarida a ranar Juma’ar da ta gabata cewa yarinyar da aka azabtar ta na wani asibitin kudi da ke cikin garin Kaduna.

Ana sa ran za a dauke ta a maida ta zuwa asibitin gwamnatin Barau Dikko domin a kula da ita. Bayan nan kuma za a gurfanar da Misis Awolala a gaban kuliya.

Za a tuhumi ma’aikaciyar ta NNPC wanda yanzu haka ta ke hannun ‘yan sanda da laifin wahalar da karamar yarinya, cin zarafi da kuma lalata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel