Gwamna Abdulrazaq ya bukaci EFCC ta binciki kudaden kananan hukumomin jiharsa
- Gwamna Abdulrazaq ya bukaci EFCC ta binciki kudaden kananan hukumomin jiharsa ta Kwara
- Gwamnan ya ce yana so a gudanar da binciken kudin ne domin wanke kansa daga zargin da wasu 'yan jihar ke yi na cewar ya karkatar da N300m
- Ya kuma tabbatar da cewa duk jami'i da aka samu da almundahana karkashin gwamnatinsa, zai girbi abunda ya shuka
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya gayyaci hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da yiwa dukiyar al'umma zagon kasa wato EFCC data gudanar da bincike na kashin kanta kan kudaden da kananan hukumomin jiharsa suka samu daga gwamnatin tarayya daga watan Mayun 2019 zuwa wannan wata.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Ilorin ta hannun babban sakataren watsa labaransa, Rafiu Ajakaye.
Ajakaye ya ce za a kafa kwamitoci daban daban domin gudanar da bincike na kashin kansu kan kudaden kananan hukumomin.
"Domin tabbatar da adalci da kasa komai akan fai fai, gwamnan ya bukaci hukumar EFCC da ta gudanar da binciken gaggawa kan kudaden da kananan hukumomin jihar suka samu tun daga ranar 29 ga watan Mayun 2019 zuwa wannan rana.
KARANTA WANNAN: 2020: Mutane 9 da zasu nemi aikin 'yan sanda da mutane 8 da basu cancanta ba
"Haka zalika, gwamnan zai kafa kwamiti a cikin karamin lokaci domin yin duba kan wannan matsalar. Za a sanar da mambobin kwamitin da kuma ka'idojin aikin nasu nan ba da jimawa ba.
"Wannan binciken za a gudanar da shi ne domin tabbatarwa duniya cewar gwamnatin jihar mai ci bata taba ko kwabo daga asusun kananan hukumomi ba.
"Babu wani tsoro da gwamnati zata ji, kamar yadda babu wani abu da zata boye.
"Domin tabbatar da adalci da bin diddigi, gwamnan ba zai tsaya akan hukumar EFCC kadai ba, zai kafa wani kwamiti wanda za a dauko mambobinsa daga bangarori daban daban domin suma suyi bincike kan kudaden kananan hukumomin, yadda aka kashe kudaden da kuma fallasa wadanda suka yi badakalar kudin idan har aka samu hakan.
"Gudanar da binciken ya zama dole la'akari da cewa akwai zarge zargen da wasu a jihohin ke yi na cewar gwamnatin jihar ta karkatar da akalla N300m daga asusun kananan hukumomin jihar," a cewar Ajakaye."
Ajakaye ya ce gwamnati mai ci a yanzu a jihar taga bukatar gudanar da binciken domin kawo karshen cece kuce, kasancewar ita gwamnati an gina ta ne akan yarda da aminci.
"Haka zalika, gwamnan jihar ya roki majalisar dokokin jihar da suka hada da zababbun wakilan al'umma da su gudanar da taron jin ba'asin al'umma kan wannan lamari.
"Gwamnan ya bayar da tabbacin cewa ba za a same shi da hannu a karkatar da kudi ko handame kudaden gwamnati ba.
"Har yanzu yana kan matsayarsa, da ya cimmawa tun yana a cikin jam'iyyar CPC, na cewar akwai bukatar baiwa kananan hukumomi 'yancin cin gashin kansu, ba tare da gwamnatin jihar ta tsawwala masu ba.
"Ya kuma tabbatar da cewa duk wani jami'i da aka samu da almundahana ko sama da fadi da kudaden al'umma karkashin gwamnatinsa, zai girbi abunda ya shuka kamar yadda shari'a zata tanadar," a cewar Ajakaye.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng