Take umarni na zai sa ka fuskanci hukunci mai tsauri - Keyamo ga DG NDE

Take umarni na zai sa ka fuskanci hukunci mai tsauri - Keyamo ga DG NDE

Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da aikin yi, ya ja kunnen Nasir Ladan, darakta janar na hukumar daukar aiki ta kasa (NDE) a kan irin abinda zai iya fuskanta na hukuncin idan har ya take umarni daga ma'aikatarsa a kan shirin ayyuka na musamman.

Majiyoyi da dama sun tabbatar da wannan jan kunnen da aka mika ga NDE.

The Cable ta ruwaito yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa Keyamo damar fara aiwatar da shirin daukar ayyukan wanda majalisar dattawa ta dakatar.

Ministan da 'yan kwamitin kwadago na majalisar dattawa sun yi musayar kalamai a kan kokarin 'yan majalisar na tsara yadda za a dibi ma'aikatan.

Keyamo ya bukaci kwamitin da su daina shiga shirin duk da sun riga sun fara sabon shiri da darakta janar na NDE wajen yadda za a diba ma'aikatan 774,000.

Take umarni na zai sa ka fuskanci hukunci mai tsauri - Keyamo ga DG NDE
Take umarni na zai sa ka fuskanci hukunci mai tsauri - Keyamo ga DG NDE Hoto: The Cable
Asali: UGC

The Cable ta gano cewa ministan ya mika wasikar umarnin nan ne ga shugaban NDE bayan umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bashi na ci gaba da shirin daukar aikin.

Ya bukaci darakta janar din da ya tsayar da duk wani shirin da yake tare da kwamitin majalisar dattawan.

Ya sake bukatarsa da ya gujewa yin wani aiki da bai samu umarni daga gareshi ba kai tsaye.

A halin da ake ciki, Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin daukar ma’aikta na musamman da majalisar dokoki ta dakatar.

Gwamnatin ta sanar da kaddamar da shirin ta shafinta na Twitter a ranar Talata, 14 ga watan Yuli.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ‘yan kasuwa 3 da wasu mutum biyu a Taraba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da shirin wanda ma’aikatar kwadago ke jagorantar, daga cikin matakan rage radadin annobar korona.

Za a dauki mutum 1,000 daga kowani karamar hukuma 774 da ke kasar, sannan kwamitocin jiha za su kula da shirin.

“An kaddamar da kwamitocin zaben ma’aikatan na jiha kuka sun fara aiki,” cewar gwamnatin tarayya ta shafinta na Twitter.

Keyamo ya yi cacar baki da majalisar dattawa a kan cewar su za su tsara yadda daukar aikin za ta kasance.

Kwamitin majalisar tarayya a kan kwadago ya dakatar da fara diban aikin sakamakon hatsaniyar da ta shiga tsakaninsu da karamin ministan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel