2020: Mutane 9 da zasu nemi aikin 'yan sanda da mutane 8 da basu cancanta ba

2020: Mutane 9 da zasu nemi aikin 'yan sanda da mutane 8 da basu cancanta ba

Rundunar 'yan sandan Nigeria a ranar Asabar ta sanar da fara daukar ma'aikata a rundunar rukunin shekarar 2020. Kakakin rundunar Frank Mba ya sanar da hakan yana mai cewa rundunar zata dauki mutanen da suka cancanta a mukamin kwanstabul, daga watan Yuli zuwa watan Agusta.

Frank Mba ya ce za a gudanar da matakan daukar aikin ne a yanar gizo inda ya bukaci masu son neman aikin da su ziyarci adireshin hukumar www.policerecruitment.gov.ng domin cike dukkanin bayanan da ake bukata.

Mba ya yi nuni da cewa dole ne masu son neman aikin da suka wasu ka'idoji da ke zayyane a shafin hukumar na yanar gizo, inda za a gayyaci wadanda suka yi nasara zuwa tantancewa ta zahiri a manyan ofisoshin hukumar dake fadin jihohin kasar da suka hada babban ofishin hukumar na Abuja, daga ranar 24 ga watan zuwa 30 ga watan Agusta 2020.

Mai magana da yawun rundunar ya ce za a manna sunayen wadanda suka samu nasarar tantancewar a manyan jaridu na kasa a ranar 14 ga watan Satumba 2020 da kuma shafin hukumar na yanar gizo.

KARANTA WANNAN: Likitoci 35 sun kamu da cutar COVID-19 a jihar Kwara - NMA

2020: Mutane 9 da zasu nemi aikin 'yan sanda da mutane 8 da basu cancanta ba
2020: Mutane 9 da zasu nemi aikin 'yan sanda da mutane 8 da basu cancanta ba
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta tattara bayani kan rukunin mutane da suka cancanci neman aikin da kuma rukunin mutanen da basu cancanta ba.

Mutanen da suka cancanci neman aikin 'yan sanda na shekarar 2020

Ga duk wanda ke son neman aikin 'yan sanda a shekarar 2020 dole ne ya kasance mai sha'awar aikin, daga nan kuma ya kasance ya cike sharuddan da ke kasa;

  • Dole ka kasance asalin d'an Nigeria a haihuwa, da kuma mallakar lambar shaidar zama dan kasa (NIN)
  • Dole ka samu makin 'credit' a darussa biyar na jarabawar kammala makarantar sakandire, kuma ya zamana cewa ba ka zarce zana jarabawar sau biyu ba na WASSCE, GCE, NECO ko NABTEB, amma dole sai da 'credit' a darussan Turanci da Lissafi.
  • Dole shekarunka ya kasance daga shekaru 17 zuwa 25
  • Dole ka kasance mai cikakkiyar lafiya, da suka hada da lafiyar kwakwalwa da kwarin jiki, sannan tsayinka ya kai mita 1.67 ga namiji, amma mita 1.64 ga mace.
  • Akwai bukatar fadin kirjinka ya kai santimita 86 wato inci 34, ko fadin kafada ga maza.
  • Ga mata, ki tabbata baki dauke da ciki a lokacin da zaki nemi wannan aiki.
  • Ka tabbata babu bakadalar kudi a kanka
  • Ka buga takardar da ka cike bayananka a shafin hukumar na yanar gizo,tare da na wanda ya tsaya maka, sannan ka mika takardun a lokacin zana jarabawar da kuma tantancewa, sannan ka kai cibiyar daukar aikin.
2020: Mutane 9 da zasu nemi aikin 'yan sanda da mutane 8 da basu cancanta ba
2020: Mutane 9 da zasu nemi aikin 'yan sanda da mutane 8 da basu cancanta ba
Asali: Depositphotos

A hannu daya kuwa, akwai rukunin mutanen da basu cancanci neman aikin 'yan sandan ba, koda kuwa sun cike bayanansu a shafin hukumar na yanar gizo, ba zasu wuce matakin tantancewa na zahiri ba.

Mutanen da basu cancanci neman aikin 'yan sanda na shekarar 2020 ba

  • Mutumin da cin abinci ke masa wahala sakamakon ciwon hakora ko haba
  • Mutumin da ke da matsala a guiwarsa
  • Mutumin da ke da gwamammiyar kafa
  • Mutumin da ke da matsala wajen jawabi ko magana
  • Mutumin da ke da guiwa mai lankwasa - ma'ana, bandararriyar guiwar da bata mikewa koda mutum ya tashi tsaye
  • Mutumin da ke fama da lalura a hannunsa
  • Mutumin da ke matsalar idanuwa, wanda baya gani sosai
  • Mutumin da ya rasa wani sashe daga jikinsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel