WAEC 2020: Gwamnatin Tarayya ba ta da hurumin yanke hukunci a kan makarantu masu zaman kansu na gwamnatocin jihohi - Ministan Ilimi

WAEC 2020: Gwamnatin Tarayya ba ta da hurumin yanke hukunci a kan makarantu masu zaman kansu na gwamnatocin jihohi - Ministan Ilimi

- Gwamnatin Najeriya ta fayyace maganar da tayi game da hukuncin hana makarantun sakandire na gwamnatin tarayya daga rubuta jarabawar WAEC a wannan shekara

- Karamin ministan ilimi ya ce gwamnatin tarayya ba ta da hurumin yanke hukuncin hana makarantu masu zaman da na gwamnatin jihohi zana jarabawar a bana

- Ana iya tuna cewa, a baya bayan nan ne gwamnatin ta sanar da cewa makarantun sakandire da ke karkashin kulawarta ba za su zana jarabawar WAEC ba bana

Bayan sanarwar da gwamnatin tarayya ta yi na hana makarantun sakandire rubuta jarabawar WAEC a wannan shekara, a yanzu ta fayyace ainihin abin da sanarwar ta kunsa.

Gwamnatin ta sanar da cewa ba ta da ikon hana makarantu masu zaman kansu da na gwamnatocin jihohi zana jarabawar WAEC a bana.

Gwamnatin ta ce dukkanin makarantun da ba sa karkashin gudanarwarta, ganin damar su ne su yanke nasu hukuncin na zana jarabawar a bana ko kuma sabanin haka.

Karamin Ministan Ilimi; Chukwuemeka Nwajiuba
Karamin Ministan Ilimi; Chukwuemeka Nwajiuba
Asali: UGC

Karamin minsistan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, shi ne ya yi wannan karin haske yayin zaman kwamitin fadar shugaban kasa mai yaki da cutar korona da aka gudanar a ranar Litinin cikin birnin Abuja.

Idan ba a manta ba, a baya bayan nan ne ministan ilimi, Mallam Adamu Adamu, ya sanar da cewa daliban makarantun sakandire na gwamnatin tarayya ba za su rubuta jarabawar WAEC ba a bana.

Sanarwar da Mallam Adamu ya fitar, ya ce makarantun sikandire na gwamnatin tarayya ba za su rubuta jarrabawar ba ta bana wadda aka kayyade za a gudanar daga ranar 5 ga watan Agusta zuwa 5 ga Satumba.

KARANTA KUMA: A lokacin da nake shugaban kasa ban bi son kaina ba - Obasanjo

Ministan yayin kiran hukumar mai shirya jarabawar kare karatun sikandare a Yammacin Afrika da ta dakatar da jarabawar a bana, ya kuma nemi gwamnatin jihohi su yi koyi da hukuncin da aka yanke.

Mallam Adamu ya ce gwamnatin ta yanke shawarar hakan ne a dalilin yadda likafar annobar covid-19 ke ci gaba babu sassauci.

Sai dai a yayin da Mista Nwajuiba ya ke karin haske, ya ce gwamnatin ba ta da hurumin zartar da wannan hukunci a kan gwamnatocin jihohi kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya yi musu tanadi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: