Kwankwasiyya: Buhari ya bawa Rabi'u Suleiman mukami mai tsoka

Kwankwasiyya: Buhari ya bawa Rabi'u Suleiman mukami mai tsoka

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da sake kunshin wakilan da ke zaman mamba a bod din hukumar NLNG (Nigeria Liquified Natural Gas) da BGT (Bonny Gas Transport Limited).

Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva.

Sabbin mambobin bod din LNG sun hada da; Edmund Daukoru a matsayin shugaba, sai Henry Ikem-Obih, Rabiu Sulaiman, Bitrus Nabasu da kuma shugaban NNPC, Mele Kyari, a matsayin mambobi.

Rabiu Sulaiman tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano ne a lokacin mulkin tsohon gwamna,, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.

Sai dai, tsohon sakataren gwamnatin ya bar tafiyar Kwankwasiyya a jam'iyyar PDP tare da komawa gidan gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a jam'iyyar APC.

A bangaren BGT Ltd, Edmund Daukoru zai kasance shugaba sai mambobinsa da suka hada da; Doyin Akinyanju, Abdul Abba, Bitrus Nabasu, da Mele Kyari.

Kwankwasiyya: Buhari ya bawa Rabi'u Suleiman mukami mai tsoka
Rabiu Suleiman yayon komawa jam'iyyar APC
Asali: Twitter

A cewar Mista Sylva, mambobin bod din da aka sauya an nadasu ne tun shekarar 2005, a saboda haka akwai bukatar nada sabbi domin samun sabon tunani wajen gudanar da harkokin kamfanonin NLNG da BGT mallakar gwamnati.

DUBA WANNAN: Ban yi wa Buhari ta karkashin kasa ba lokacin da nake aiki da Jonathan - Dasuki

Ya jinjinawa tsofin shugabanni da mambobin bod din NLNG da na BGT bisa nasarorin da suka samu yayin aikinsu.

Ya yi mu su fatan alheri tare rokar musu koshin lafiya a yayin da zasu tunkari wasu al'amuran a rayuwarsu.

"Ga sabbin mambobi, ina tayaku murnar zabenku da kuma tabbatar da ku bayan gamsuwa da gogewarku, kimarku da kuma kwarewarku ta aiki.

"Ina kira gareku da ku yi amfani da dukkan nagartarku, wacce saboda ita aka daukeku, wajen sauke nauyin da aka dora muku tare da zama ma su kare akidun gwamnatin shugaba Buhari," a cewar Sylva.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel