Ministan shari'a zai iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 5 - Lauya
Kabir Akingbolu, lauya mai rajin kare hakkin bil adama, ya ce ministan shari'a, Abubakar Malami, ya na cikin hatsarin fuskanatar hukuncin daurin shekaru biyar bisa bayar da izinin siyar da gangunan man fetur mallakar gwamnatin tarayya.
Lauyan ya yi zargin cewa Malami ya bayar da umarnin sayar da kadarorin ne ba bisa ka'ida ba, bayan jami'an tsaro sun kwatosu daga hannun barayin man fetur a yankin Neja - Delta.
Wasu rahotanni sun wallafa wata takarda da ke nuna cewa Malami ya bayar da umarnin sayar da wasu manyan gangunan danyen man fetur ga wani kamfani bayan an kwacesu daga hannun barayin da ke fasa bututun NNPC.
Rahotannin sun bayyana cewa Malami ya bawa wani kamfani mai suna 'Omoh-Jay' umarnin sayar da danyen man fetur din da ke cikin gangunan duk da ana tuhumar kamfanin da zargin barnatar da metrik ton 12,000 na danyen man fetur a shekarar 2009.
Da ya ke kare kansa, Malami ya ce bai aikata wani laifi ba don ya bayar da umarnin a yi gwanjon danyen man gwamnati.
A cewar ministan, sashe na 36 (5) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ya bawa kamfanin Omoh -Jay damar shiga ciniki ko dillancin man fetur a Najeriya saboda ya na da rijista da gwamnati kuma har yanzu kotu ba ta sameshi da laifi ba a tuhumar da ake yi ma sa.
Amma, a cikin wani jawabi da Lauya Akingbolu ya fitar ranar Litinin, ya ce Malami ya 'wuce gona da iri' ta hanyar yin gaban kansa wajen bayar da izinin sayar da kadarar gwamnatin tarayya ba tare da samun izini daga hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ba.
DUBA WANNAN: Binciken badakalar EFCC: Magu ya sake bayyana gaban kwamiti
Ya ce sashe na 31 (4) na kundin hukumar EFCC ya bawa ministan shari'a ikon tsara dokokin da EFCC za ta yi aiki dasu kafin yin gwanjon kadarar gwamnati, amma doka ba ta bashi ikon bayar da izinin yin gwanjon kadarar gwamnati ba.
"Bashi da iko a karkashin sashe na 174 na kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma a karkashin kundin hukumar EFCC na shekarar 2004," a cewarsa.
Lauyan ya bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sa babban sifeton rundunar 'yan sanda ya kamma Malami domin gurfanar da shi a gaban kotu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng