Yadda na yaki cin hanci, na tarawa Najeriya makudan biliyoyi - Ngozi Okonjo-Iweala

Yadda na yaki cin hanci, na tarawa Najeriya makudan biliyoyi - Ngozi Okonjo-Iweala

Dakta Ngozi Okonjo-Iweala, tsohuwar ministar kudi a lokacin tsofin shugabannin kasa; Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan, ta yi waiwaye adon tafiya a kan yadda ta bullo da hanyoyin yaki da cin hanci.

Tsohuwar ministar, wacce yanzu ke aiki da wata hukumar lafiya ta duniya, ta bayyana yadda ta rike tare da jan akalar al'amuran da suka shafi gina tattalin arzikin kasa a lokacin da ta ke kan mulki a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2006 da tsakanin 2011 da 2015.

Ta bayyana cewa ta mayar da hanakali wajen fitar da bayanai domin dakile cin hanci tare da tarawa kasa dumbin biliyoyi da aka yi amfani dasu a gwamnati.

"Akwai bukatar a samar da kayan aikin kiwon lafiya kafin a samar da rigakafi, akwai bukatar tallafi ya isa wurin wadanda suka fi bukatarsa.

"A kasashe da dama an samu rahotannin cin hanci da almundahana da harkalla a sha'anin bayar da kwangilar kayan tallafi.

Yadda na yaki cin hanci, na tarawa Najeriya makudan biliyoyi - Ngozie Okonjo Nweala
Yadda na yaki cin hanci, na tarawa Najeriya makudan biliyoyi - Ngozie Okonjo Nweala
Asali: UGC

"Gaggawa da cin hanci a bangaren gwamnati sun haifar da bayar da kwangiloli ga 'yan kwangilar gan - gan da na bogi.

"Matukar gwamnati ta na son magance harkalla wajen sayen kayayyaki, dole ta ke fitar da bayanan kwangila da na 'yan kwangila domin jama'a su sa ido a kansu wajen tabbatar da cewa ba a karkatar da hakkinsu ba.

"Yanzu ne lokacin da yafi kamata gwamnati ta ke fitar da bayanan yadda ta ke kashe kudade domin nuna cewa suna tausayawa jama'a halin kuncin da ake ciki.

DUBA WANNAN: Buhari ya taya Usman murnar zama shagon gasar damben UFC

"Yin hakan zai kara yarda tsakanin gwamnati da jama'ar da ta ke mulka.

"Lokacin da nake aiki a matsayin ministar kudi, mun yi aiki tukuru domin wajen fitar da bayanai tare da dakile cin hanci.

"Duk da yin hakan ba abune mai sauki a karkashin irin gwamnatinmu ba, mun yi hakan domin dakile cin hanci ta hanyar bawa jama'a damar bin diddigin yadda ake kashe kudadensu da suka biya haraji

"Kuma ta wannan hanyar na tarawa gwamnati biliyoyin kudin da aka yi amfani da su domin rike tattalin arzikin kasa," kamar yadda Ngozi ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel