Yanzu-yanzu: Minista ta bayyana adadin wadanda suka nemi aikin N-Power
- 'Yan Najeriya miliyan 4.4 sun nuna ra'ayinsu kan neman aikin N-Power
- An gano hakan ne daga kididdigan yawan mutanen da suka nemi aikin a shafin yanar gizo na diban ma'aikatan zuwa yanzu
- Ma'aikatar walwala da jin dadin 'yan kasa ta bude shafin na daukar ma'aikatan kashi na uku a ranar 26 ga watan Yunin 2020
Rahoto ya nuna cewa a halin yanzu, shafin yanar gizo na diban ma'aikatan N-Power ya samu mutane miliyan 4.48 da suka nuna bukatar aikin.
Ma'aikatar walwala da jin dadin 'yan kasa ta bude shafin na daukar ma'aikatan kashi na uku a ranar 26 ga watan Yunin 2020.
Bayan kwana 16 da bude shafin karbar masu bukatar aikin, sama da mutum miliyan 4 sun nuna bukatar su.
Kamar yadda ma'aikatar ta sanar, ta ce mutum 400,000 za ta dauka don aiki a kashi uku na N-Power a karon karshe.
Ministar ma'aikatar walwala da jin kan 'yan kasa, Sadiya Farouq ce ta bayyana yawan wadanda suke bukatar aikin da yawan wadanda za su diba.
KU KARANTA KUMA: Wa'iyazubillah: Tsoho dan shekara 60 ya lalata wata karamar yarinya
Ta ce: "Tawagata da ni kaina muna ci gaba da kokarin ganin tafiyar kashin farko da na biyu na N-Power. A yau kwanaki 16 da bude shafin kuma mun samu mutum 4.48 da suka nuna bukatar aikin."
Idan za ku tuna a shekarun baya fadar shugaban kasa ta bayyana yadda ta kashe Naira Biliyan 109 wajen inganta rayuwar marasa galihu a kasar nan.
Mai magana da yawun Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne yayi wannan jawabi.
Laolu Akande yace Gwamnatin Buhari ta ware kusan Tiriliyan guda a 2016 da 2017 wajen ciyar da yaran makaranta da kuma aikin N-Power na matasa.
Bayan nan kuma an ba marasa hali N5000 domin agaza masu, ban da mata da aka ba jari.
An dai kashe sama da Biliyan 100 a wa'adin mulkin Buhari na farko wajen wannan tsare-tsare na gwamnatinsa.
An ciyar da yaran makaranta sama da Miliyan 246 a Jihohi da dama a wannan Gwamnati inji Fadar Shugaban kasar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng