Wata sabuwa: Ana tuhumar Magu a kan gidaje 332 da jiragen ruwa na man fetur 2
Rahotanni sun kawo cewa an sake zargin dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahhim Magu, da kin bayar da cikakken bayani kan kadarori 332 da suka bata cikin 836 da aka kwato a watan Maris, 2018.
Wani rahoto daga kwamitin bayani a kan kudaden da aka samo (PCARA) ya bayyana cewa hukumar EFCC ta kasa bada bayanin wasu kadarorin biliyoyin naira.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai ya sanar, rahoton ya ce an samu asara da tagayyarar kadarori, motoci da sauran su duk da aka samo daga mahandama.
Ya kara da nuna damuwarsa kan yadda aka kasa adana dukiyoyin da gane darajarsu ta fuskacin tattalin arziki.
Ya bayyana cewa an samo wasu daga cikin kadarorin fiye da shekaru 15 da suka gabata amma aka barsu a wargaje.
"Wani ci gaba mai matukar bada haushi shine yadda wasu jiragen ruwa biyu dankare da man fetur suka yi batan dabo karkashin shugabancin mukaddashin shugaban hukumar EFCC.
"An bar jiragen ruwan sun nitse a teku duk da jan kunnen da sojojin ruwa suka dinga yi a kai da bukatar a kwashe kayayyakin man fetur da ke ciki.
"Jimillar kudin kadarorin da suka bace a sakamakon nuna halin ko in kulan sun kai miliyoyin daloli.
"Har a halin yanzu dakataccen mukaddashin shugaban hukumar EFCC ya kasa bada bayanin abinda ya faru da jiragen ruwan," rahoton yace.
Pmnews ta tattaro cewa ana kara zargin shugaban EFCC da yin sama da fadi da wasu gidaje wadanda aka kwace.
Kamar yadda aka gano, Magu tare da wasu jami'an EFCC na amfani da dukiyar EFCC suna azurta kansu.
KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: 'Yan bindiga sun barmu da zawarawa 500 da marayu 1,600 - Sarkin Ruman Katsina
"Da yawa daga cikin kadarorin da aka samo an siyar da su ba tare da sani hukumomin da suka dace ba. Wasu kuwa jami'an me suka dauka yayin da wasu aka siyar da su a arha ga masoya da abokai.
"Daga nan an yi amfani da wadannan kudaden don siyan wasu kadarorin da sunan makusantan shugaban hukumar," rahoton ya kara da cewa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng