Korona ta harbi sabbin mutane 664 a Najeriya
A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na tuwita tun bayan bullar annobar korona, ta sanar da cewa karin sabbin mutane 664 ne aka tabbatar da cewa kwayar cutar covid-19 ta sake harba a fadin Najeriya.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC tawallafa a shafinta a daren ranar Asabar, 11 ga watan Yuli, 2020.
NCDC ta fitar da jerin jihohi da jimillar ma su dauke da kwayar cutar a kowacce jiha kamar haka;
Lagos-224
FCT-105
Edo-85
Ondo-64
Kaduna-32
Imo-27
Osun-19
Plateau-17
Oyo-17
Ogun-17
Rivers-14
Delta-11
Adamawa-10
Enugu-7
Nassarawa-6
Gombe-3
Abia-3
Ekiti-3
NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:46 na daren ranar Asabar akwai jimillar mutane 31987 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.
DUBA WANNAN: 'Kisan girmamawa': Wani miji ya kashe matarsa ta hanyar jefeta da duwatsu
An sallami mutane 13103 bayan an tabbatar da samun saukinsu, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 724.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng