Fasinjoji sun lakaɗawa direba duka ya mutu saboda tukunkumin fuska

Fasinjoji sun lakaɗawa direba duka ya mutu saboda tukunkumin fuska

Wani direban mota da fasinjoji suka yi wa mugun duka a kasar Faransa saboda ya ce su saka takunkumin fuska don kare yaduwar coronavirus ya mutu kamar yadda iyalansa suka bayyana.

Mutuwarsa ya janyo hankalin mutanen kasar musamman shugabanin gwamnati da yan siyasa wadda suka yi tir da abinda fasinjojin da suka kai masa hari suka aikata.

Philippe Monguillot, mai shekara 59 ya samu matsala a kwakwalwarsa bayan harin da aka kai masa a garin Bayonne da ke kudu masa yammacin kasar kuma ya mutu a ranar Jumaa bayan iyalansa sun ce likitocin su kyalle shi ya mutu ya huta.

Fasinjoji sun lakaɗawa direba duka ya mutu saboda tukunkumin fuska
Fasinjoji sun lakaɗawa direba duka ya mutu saboda tukunkumin fuska. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Umar: Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan sabon shugaban riko na EFCC

"Mun yanke shawarar mu kyalle shi ya huta. Likitocin suma sun goyi bayan hakan," kamar yadda diyarsa Marie ta shaidawa AFP

An gurfanar da mutane biyu a kotu bisa tuhumarsu da yunkurin kisa kuma mai shigar da kara Jerome Bourrier ya shaidawa AFP cewa zai canja tuhumar zuwa kisar gilla bayan mutuwar Monguillot.

Farai ministan kasar Faransa Jean Castex ya yi taaziya bisa rasuwar Monguillot

"Jamhuriyar mu za ta rika tunawa da shi a matsayin dan kasa na gari kuma ba za ta manta da shi ba. Doka za ta hukunta wadanda suka aikata wannan mummunan abin," ya rubuta a Twitter.

Ministan harkokin cikin gida Gerald Darmanin wanda ya gana da wasu direbobin bus na garin Bayonne a ranar Asabar don tattaunawa kan inganta tsaronsu ya bayyana abin a matsayin "mummunan aiki."

Ya kara da cewa, "ragwayen da suka aikata wannan za su fuskanci hukunci."

Iyalan Monguillot sun shirya wata tattaki don karrama shi a ranar Laraba, inda suka fara daga wurin shiga mota da harin ya faru.

Abokan aikinsa sun ki komawa aiki amma za su fara aiki a ranar Litinin bayan an inganta tsaro a cewar wani direba Keolis.

Za a samar da jamian tsaro a cikin manyan motoccin bus a Bayonne da kewaye.

Ofishin masu bincike sun ce za a gurfanar da wasu saboda kin taimakawa mutumin da ke cikin hatsari sai wani kuma da ya yi yunkurin boye wanda ake zargi.

Mutum biyu da ake tuhumma da aikata laifin kisar masu shekaru 22 da 23 damma sanannu ne ga yan sandan jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel