Maimakon haska bidiyon karbar dalan Ganduje, da aikin da ka yiwa mutane ka haska - Ize-Iyamu ya caccaki Obaseki

Maimakon haska bidiyon karbar dalan Ganduje, da aikin da ka yiwa mutane ka haska - Ize-Iyamu ya caccaki Obaseki

Dan takaran gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC, Fasto Osaze Ize-Iyamu ya caccaki gwamnan jihar, kuma abokin hamayyarsa Godwin Obaseki.

Ya ce gwamnan ya nuna rashin hankali bisa haska bidiyon karbar Dalan Ganduje kan allon talla a Ring Road, cikin babbar birnin jihar, Benin.

A jawabin da Diraktan labaran yakin neman zabensa, John Mayaki, ya saki, ya ce abin kunya ne kuma munafurci ne abinda Obaseki yayi.

Ya ce hakan ya nuna cewa gwamnan bai da wani aikin kwarai da zai iya nuna wa al'umma jihar da ya tsinana, shi yasa yake daura hoton wani gwamna na wata jiha daban don cin mutuncinsa.

Yace: "Ya bayyana karara ga kowa a jihar da ko ina cewa gwamnan jihar Edo, Mr Godwin Obaseki, da jam'iyyarsa na masu karban haraji ba su wani aikin da zasu iya kamfe da shi."

"Idan ba haka ba, maimakon bannatar da kudin gwamnati wajen kokarin cin mutuncin gwamna Umaru Ganduje na jihar Kano, da ya nunawa mutan Edo abubuwa masu muhimman da samu nasarar yi."

"Kawai rashin wayo da munafurci ne irin wannan ne ya sa gwamnatin Obaseki ta gaza."

"Idan Obaseki bai da wani abin 'a zo a gani' da zai nunawa mutan jihar Edo fiye wannan yarintan da kokarin bata suna, kawai ya natsu zuwa 19 ga Satumba da za'a fitittikesa daga ofis."

Maimakon haska bidiyon karbar dalan Ganduje, da aikin da ka yiwa mutane ka haska - Ize-Iyamu ya caccaki Obaseki
Ize-Iyamu ya caccaki Obaseki
Asali: UGC

Legit ta kawo muku rahoton cewa yayinda ake shirye-shiryen zaben gwamna a jihar Edo, wanda za a gudanar a watan Satumba, wasu sun sanya wani bidiyo a katon allon majigi inda masu tafiya a kafa da mota za su iya gani.

Bidiyon yana nuna gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, yana cusa daloli cikin aljihunsa.

Wani mai rajin kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju ya wallafa bidiyon a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 9 ga watan Yuli.

Za ku tuna cewa a shekarar 2018 gwamnan Kanon ya fada a wata badakala na zargin aikata rashawa, bayan wani bidiyo da ya billo ya hasko shi yana zuba daloli a aljihu wanda aka ce cin hanci ne ya karba daga yan aikin kwangila.

Kalli bidiyon:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel