Mazauna Dorowan Babuje na korafi a kan harin 'yan ta'adda

Mazauna Dorowan Babuje na korafi a kan harin 'yan ta'adda

Mazauna kauyen Dorowan Babuje ta karamar hukumar Barikin Ladi a jihar Filato, sun koka da yawaitar hare-haren 'yan ta'adda da 'yan fashi da makami.

Kamar yadda shugaban matasa Abdullahi Garba ya sanar, 'yan ta'addan su kutsa yankin inda suke tsorata jam'a ballantana lokacin bukukuwa. Su kan balle gidan jama'a su shiga.

Garba ya ce 'yan fashi da makamin kan balle shaguna tare da karbar kudi daga masu shagunan. Ya ce hakan ya dade yana faruwa da su.

"Bamu iya bacci idonmu biyu a rufe. Mutane na tsoron abinda zai iya faruwa a kowanne lokaci.

"A kowanne lokaci aka kawo mana hari, jama'a kan dinga gudun ceton rai saboda maharan kan kutso da bindigogi," shugaban matasan yankin ya sanar.

Daya daga cikin wadanda aka kai wa harin kuma mamallakin shago, mai suna Abubakar Khamis ya ce: "Ina cikin kasuwanci na lokacin da 'yan bindiga suka kawo min hari a shagona. Sun amshe dukkan kudin da nayi ciniki a ranar.

"Hankalinmu baya kwance a yankin saboda har da rana tsaka 'yan bindigar ke kawo hari."

Mazauna Dorowan Babuje na korafi a kan harin 'yan ta'adda
Mazauna Dorowan Babuje na korafi a kan harin 'yan ta'adda. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotuna: Sojoji sun halaka 'yan bindiga a Sokoto, Katsina da Zamfara, sun kwato dabbobi 651

Shugaban matasan ya yi kira ga gwamnatin jihar da sauran jami'an tsaro, da su gaggauta kawo musu dauki a kan halin da suke ciki.

A lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Ubah Gabriel, ya ce rundunar bata samu wani rahoto a kan abinda ke faruwa.

Amma ya yi alkawarin tuntubar ofishin 'yan sandan yankin don jin karin bayani.

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun kashe hakimin garin Bajida da ke karamar hukumar Fakai ta jihar Kebbi, Alhaji Musa Muhammad Bahago, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Yayan hakimin da aka kashe, Alhaji Umar Muhammad, ya yi bayanin cewa an kashe kaninsa a ranar Laraba tsakanin karfe 4 zuwa 6 na yamma a yayin da yake kan hanyar komawa gidansa da ke garin Zuru.

"Ya rasu yana da shekaru 56 kuma ya bar mata hudu da 'ya'ya masu tarin yawa," Muhammad yace.

A lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Nafi'u Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.

Ya ce: "Da gaske ne kuma mun san da aukuwar lamarin mai cike da takaici."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng