Rundunar 'yan sanda za ta fara gurfanar da ma su kango a Kano

Rundunar 'yan sanda za ta fara gurfanar da ma su kango a Kano

Daga yanzu rundunar 'yan sanda za ta fara gurfanar da duk wani mai kango a jihar Kano tare da duk wanda aka kama da laifin aikata fyade a cikin kangon da ya mallaka.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna, ne ya sanar da hakan ga manema labarai a ranar Alhamis.

Ya ce rundunar 'yan sanda ta yanke wannan shawara ne bayan sakamakon rahoton bincike ya nuna cewa kaso 33.3 na laifin fyade ana aikata shi a cikin kangwayen jama'ar da a kammala ginasu ba.

"Bincikenmu ya nuna cewa kaso 33.3 na laifin fyade an aikatasu ne a cikin kango da ba a kammala gininsu ba, sannan an fi lalata kananan yara a irin wadannan wurare," a cewar Abdullahi.

Ya ce bayan fitowar sakamakon binciken ne rundunar 'yan sanda ta bullo da tsarin fadada sintirin da jami'anta ke yi zuwa kangwaye da ke lungun da sakon jihar Kano.

Rundunar 'yan sanda ta gargadi ma su kangwaye a jihar Kano su karasa ginasu domin kaucewa gurfana a gaban kotu da laifin taimakon ma su laifi, musamman aikata fyade a kan kananan yara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel