Wasan kwaikwayo: NFVCB za ta kama wadanda su ka tsara shirin ‘Ife’

Wasan kwaikwayo: NFVCB za ta kama wadanda su ka tsara shirin ‘Ife’

Hukumar NFVCB da ta ke tace wasannin kwaikwayo a Najeriya ta ce za ta cafke wadanda su ka shirya wasan fim dinnan na ‘Ife’ muddin aka fitar da shirin a kasuwa.

NFVCB ta ce za ta cafke masu wannan shiri da bai riga ya fito ba tukuna, idan har su ka fitar da fim din ba tare da hukumar ta tace sa ba.

A jiya Laraba, darektan hukumar kasar watau Mista Adedayo Thomas ya fadawa ‘yan jarida cewa: “Dokar kasa ta haramta bayyana wasu abubuwa.”

Jaridar Daily Trust ta rahoto Adedayo Thomas ya na cewa ba za su bari a fito da wannan fim ga ‘yan Najeriya ba.

“Muddin a Najeriya ne, za mu sauke shi.”

Shararriyar ‘yar fim Uyai Ikpe-Etim mai shekaru 45 ce ta bada umarni wajen tsara wannan fim da ya jawo ce-ce-ku-ce tun kafin ya bayyana.

KU KARANTA: Ahmed Musa ya yabi Mai dakinsa bayan sun yi shekara 3 da aure

Wasan kwaikwayo: NFVCB za ta kama wadanda su ka tsara shirin ‘Ife’
Shirin 'Ìfé' Hoto Instagram/@ife_movie
Asali: Twitter

A wani bangare guda, wadanda su ka shirya wannan fim na ‘Ife’ da bai ka ga zuwa kasuwa ba, sun ce babu wani abin batanci a cikin fim din na su.

Masu wannan fim sun ce soyayya ce kurum a cikin labarinsu ba wai batanci ko fitsarar da ta shafi madigo kamar yadda wasu ke rayawa ba.

A cewar Pamela Adie, soyayya ce za a gani a fim din da ta shirya. Hotunan da su ke yawo yanzu ba za su iya tabbatar da hakan ba.

“Kafin ka shiga wata harkar, akwai ka’idoji.”

“Menene sharudan?”

“Rashin sanin doka ba uzuri ba ne.”

Thomas ya kara da cewa: “Idan ku ka ce ku na haska fim a kan ‘yan madigo, shi kenan, ya yi.”

“Bai zo ga teburin mu ba.”

“Idan fim din ya zo kan teburin mu, za mu san cewa ga abin da za mu yi nan.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel