Jami'in ɗan sanda ya harbe ɗan kabu-kabu saboda rashin sanya takunkumin rufe fuska a Imo
A ranar Alhamis, wani mummunan tsautsayi ya auku a kwanar Banana da ke Unguwar Orlu ta jihar Imo, inda wani jami'in dan sanda ya harbe wani matashi saboda rashin sanya takunkumin rufe fuska.
Wannan lamari na takaici da ya auku da misalin karfe 3.00 na Yamma, ya janyo fushin matasa da 'yan tireda na kurkusa, inda suka yi barazanar kai hari wani ofishin 'yan sanda da ke kusa.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, an yi gaggawar tura tawagar jami'an tsaro domin tunkarar lamarin tare da kwantar da tarzomar da ta yi yunkurin tashi.
Wani mashaidin wannan lamari, ya ce daya daga cikin jami'an 'yan sanda da ke bincike a kan hanya, ya harbe matashin ɗan kabu-kabun mai shekaru 27, inda ya mutu nan take.
Mai ba da shaidar ya ce, "Wani jami’in ɗan sanda ya harbe wani ɗan Achaba da ke haye a kan babur a kwanar Banana saboda bai sanya takunkumin rufe fuska ba."
"Bayan da ɗan sandan ya tsayar da ɗan kabu-kabun, ya tambaye shi dalilin rashin sanya takunkumin rufe fuska, ba tare da an yi aune ba, sai kwatsam ya harbe shi kuma ya mutu nan take."
"Abin da ke faruwa a yanzu yana neman ya wuce gona da iri. Matasa, 'yan Achaba da kuma 'yan tireda, sun fusata tare shiga farautar jami'an 'yan sanda wanda tuni suka ranta a na kare."
"Jami'an 'yan sandan da suka rage a ofishin 'yan sandan, sun cire kakakinsu na aiki, inda suka sauya da kayansu na gida."
Sai dai yayin da kwamishinan 'yan sanda na jihar, Isaac Akinmodele, wanda ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, bai bayyana sunan jami'in ɗan sandan da ya aikata wannan fasadi ba.
KARANTA KUMA: ASUU ta fusata da yanayin ɗaukar ma'aikata masu yawa a jami'ar Bayero
Yayin bayar da tabbacin cewa lamarin bai sabule daga hannunsu ba, kwamishinan 'yan sandan ya ce "mutane na da hakkin nuna fushinsu yayin da aka kashe musu ɗan uwa."
Ya kuma ce "an sassari ɗaya daga cikin jami'an 'yan sanda da adda, wanda a halin yanzu yana kwance a gadon asibiti karkashin kulawar kwararrun lafiya."
"Na fada wa dukkan bangarorin da su kwantar da hankulansu, dole sai an fitar wa da kowa hakkinsa, domin kuwa babu wanda ya fi karfin doka."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng