Magu, Sakataren EFCC, Diraktoci sun gurfana gaban kwamitin bincike

Magu, Sakataren EFCC, Diraktoci sun gurfana gaban kwamitin bincike

Mukaddashin shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, da aka dakatar, Ibrahim Mustapha Magu, ya sake gurfanar gaban kwamitin bincike yau Alhamis.

Wannan shine kwana na hudu da Magu zai bayyana gaban kwamitin bincikensa na musamman karkashin jagorancin Alkali Ayo Isah Salami a fadar shugaban kasa dake Abuja.

A yau, Magu ya gurfana tare da Sakataren hukumar EFCC, Olanipekun Olukoyede, tare da wasu dirkatocin hukumar.

Hakazalika sabanin kwanaki uku da suka gabata, yau Lauya Magu, Abbas Shittu na tare da shi.

KU KARANTA: Abubuwa 5 da suka faru da Ibrahim Magu cikin kwanaki 4

Magu, Sakataren EFCC, Diraktoci sun gurfana gaban kwamitin bincike
Magu, Sakataren EFCC, Diraktoci sun gurfana gaban kwamitin bincike
Asali: UGC

Bayan wasu jami'an 'yan sanda da ke aiki da sashen binciken manyan laifuka (FCIID) sun birkice gidan Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFCC da shugaba Buhari ya dakatar, ya yi kwanansa na uku a tsare.

A ranar Talata, wasu jami'an FCID sun kai simame gidan Magu dake titin Abduljalil a unguwar Karu da ke wajen birnin tarayya, Abuja.

Bayan kammala zaman jiya misalin karfe 8:30 na dare, an sake mayar da shi ofishin yan sanda inda ya kwana.

Ofishin ministan Shari'a, Abubukar Malami na yiwa Ibrahim Magu wasu manyan tuhume-tuhume 10.

Ga jerin tuhume-tuhume 10 cikin 22 da ake yiwa Ibrahim Magu

1. Tufka da warwara wajen lissafin kudaden da EFCC ta kwato hannun barayin gwamnati

2. Ikirarin cewa N539bn aka kwato maimakon N504bn

3. Rashin biyayya ga ofishin Antoni Janar na tarayya,Abubakar Malami

4. Rashin gabatar da isassun hujjoji domin dawo da Diezani Alison-Madueke Najeriya

5. Bata lokaci wajen binciken kamfanin P&ID wanda ahakan ya kai ga rikicin da ake a Kotu yanzu

6. Kin bin umurnin kotu na sakin asusun wani tsohon diraktan banki kimanin N7bn

7. Bata lokaci wajen daukan mataki kan jiragen ruwa biyu da hukumar Sojin ruwa ta kwace

8. Fifita wasu jami'an EFCC wadanda akafi sani da 'Magu Boys' kan sauran

9. Kai wasu Alkalai kara wajen shugabanninsu ba tare da sanar da Antoni Janar ba 10. Sayar da dukiyoyin sata ga yan'wansa, abokan arziki da abokan aiki

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel