Jigo a APC ya nemi kotu ta rushe kwamitin rikon kwarya ta Buni

Jigo a APC ya nemi kotu ta rushe kwamitin rikon kwarya ta Buni

Lateef Arigbaruwo, jigo a jam All Progressive Congress (APC), daga jihar Legas ya shigar da kara a wata babban kotun tarayya da ke Legas yana neman a rushe kwamitin rikon kwarya ta jami'yyar.

Yayin taron Kwamitin Zartarwa na jami'yyar, NEC, da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ne aka rushe Kwamitin Gudanarwa ta Jami'yyar da Adams Oshiomhole je jagoranta.

Sannan aka nada Mai-Mala Buni, gwamnan jihar Yobe a matsayin shugaban kwamitin riko na jami'yyar ta APC.

An yi taron ne a dakin taron Majalisar Zartarwa ta Kasa, FEC, da ke fadar shugaban kasa a birnin tarayya Abuja.

Jigo a APC ya nemi a rushe kwamitin rikon kwarya ta Buni
Jigo a APC ya nemi a rushe kwamitin rikon kwarya ta Buni. Hoto daga The Cable
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An haifi jariri rike da na'urar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna)

A cikin karar da ya shigar mai lamba FHC/L/CS/789/2020, Arigbaruwo ya yi korafi kan taron NEC din da jami'yyar ta yi a ranar 25 ga watan Yuni.

Ya bukaci kotun ta bincika idan waadin awa 24 da aka bayar kafin taron na NEC ya yi daidai da tanadin kudin tsarin jami'yyar.

Mai shigar da karar kuma ya nemi kotun ta rushe dukkan nade naden da aka yi a taron domin a cewarsa taron haramtaciyya ce tunda a ranar 24 ga watan Yuni aka sanar da taron kuma aka yi a ranar 25 ga watan Yuni wadda hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin APC.

Yana kuma son kotu ta bayar da umurnin dakatar da mambobin kwamitin riko su dena aiki a matsayin wakilan jami'yyar.

Ya kuma bukaci kotun ta bawa Hilliard Eta, mataimakin jami'yyar APC na kasa, yankin Kudu maso Kudu ikon cigaba da jan ragamar shugabancin jam'iyyar ya kuma riko jagorancin taron NWC da NEC.

Wadanda aka yi karar su cikin takardar sun hada da jami'yyar ta APC, Victor Giadom, NEC da kuma hukumar zabe mai zaman kanta na kasa, INEC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164