Daukan ma’aikata 774,000: Adadin gurbin da za a bai wa Gwamnoni, 'yan majalisu da ministoci

Daukan ma’aikata 774,000: Adadin gurbin da za a bai wa Gwamnoni, 'yan majalisu da ministoci

Za a bai wa gwamnonin jihohi, 'yan majalisar tarayya da ministoci gurbi na musamman a ayyuka 774,000 da gwamnatin tarayya za ta dauka.

Kwamitin zaben ma'aikatan ne ya bayyana hakan a jiya Laraba yayin sanar da yadda daukar wadanda za su ci moriyar shirin za ta kama, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Shugaban kwamitin a jihar Bauchi, Sanusi Aliyu Kunde, ya sanar da hakan yayin rantsar da kwamitin na jihar.

Ya ce: "Za a bai wa gwamnoni gurbin mutum 40 a kowacce jihar. Za a bai wa sanatoci gurbin mutum 30 daga kowacce karamar hukumar da ke karkashin mazabar da yake wakilta.

"Idan babban jami'i a majalisar dattawa dan asalin jiha ne, za a bashi gurbin mutum 40 a kowacce karamar hukumar da ke mazabarsa.

"'Yan majalisar wakilai za su samu gurbin mutum 25 daga kananan hukumomi da suke wakilta. Manyan jami'ai kuwa za su samu gurbin mutum 30. Za a bai wa ministoci gurbin mutum 30 daga dukkan kananan hukumomi da ke jiharsu."

Daukan ma’aikata 774,000: Adadin gurbin da za a bai wa Gwamnoni, 'yan majalisu da ministoci
Daukan ma’aikata 774,000: Adadin gurbin da za a bai wa Gwamnoni, 'yan majalisu da ministoci Hoto: The Cable
Asali: UGC

Kunde ya kuma bayyana cewa kwamitin zai yanke hukunci kan guraben da za a ba ‘ yan majalisar dokoki na jiha.

Ya ce karamin ministan kwadago, Fetus Keyamo ne ya rantsar da shi a ranar 29 ga watan Yunin 2020 don zabar munaten a kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi.

KU KARANTA KUMA: Sunaye: Bagudu ya amince da nadin sabbin hakimai 5 a jihar Kebbi

"A takaice, za mu dauki mutum 20,000 don wannan shirin. An bukacemu da mu saka mutum 200 wandanda suka yi karatu a kowacce karamar hukuma don amfani dasu wurin kiyasi."

Kamar yadda Kunde yace, wadanda aka dauka aikin zasu yi aikin tsakanin watan Oktoba zuwa Disamban 2020 a kowacce karamar hukuma.

"Za a biya su N60,000 a watanni uku. Za a sa su kula da tituna, gidajen da ake ginawa, tsaftace birane da kauyuka, kiwon lafiya da sauran ayyukan da ake bukata a kananan hukumomin."

Kunde ya ce kamar yadda aka bai wa kwamitin umarni da tsarin aiki, babu shakka za a yi nasarar taba rayuwar 'yan Najeriya 774,000 kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng.

Asali: Legit.ng

Online view pixel